An Sake Yin Babban Rashi: Bayan Rasuwar Buhari, Mai Martaba Sarkin Ijebu Ya Mutu
- Bayan rasuwar Muhammadu Buhari, Najeriya ta sake shiga alhini yayin da sarkin Ijebu, Sikiru Adetona, ya rasu yana da shekaru 91
- Gwamna Dapo Abiodun wanda ya tabbatar da rasuwar sarkin, ya marigayin ya taimaka wajen gina kasar Ijebu da ma jihar Ogun
- Oba Adetona ya hau sarauta a 1960, ya yi mulki tsawon shekaru 65, kuma ya inganta kasarta ta fuskar ilimi, lafiya da sauran su
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ogun – Ƴan awanni bayan an sanar da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, an sake yin wani babban rashi a Najeriya
Legit Hausa ta samu rahoto cewa mai martaba sarkin ƙasar Ijebu, Oba Sikiru Kayode Adetona, ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

Source: Twitter
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya tabbatar da rasuwar sarkin a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta, a ranar Lahadi, inji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da gwamna ya ce kan rasuwar Sarkin Ijebu
A cikin sanarwar da ya fitar, Gwamna Abiodun ya ce:
"Cikin baƙin ciki nake sanar da rasuwar Mai Martaba, Oba Sikiru Kayode Adetona, sarki mai daraja ta ɗayaa na masarautar Ijebu.
"Oba Adetona ya koma ga Mahaliccinsa a yau Lahadi, 13 ga Yulin 2025, yana da shekara 91.
"Haƙika ya bar mana babban tarihi da ba za mu manta ba, domin ya taka rawar gani wajen gina ƙasar Ijebu da ke jihar Ogun da ma Najeriya gaba ɗaya."
Gwamna Abiodun ya lura cewa rasuwar sarkin ta zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke cikin jimami saboda rasuwar Buhari, wanda ya rasu a safiyar ranar a wani asibiti a Landan.
"Lallai muna cikin baƙin ciki kashi biyu; rasuwar Oba Adetona ta haɗu da rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a Ƙasar Ingila," in ji Abiodun.
Shekaru 65 na mulkin Awujale Adetona
Oba Sikiru Adetona ya hau gadon sarauta a shekarar 1960 kuma ya yi mulki tsawon shekaru 65. Ya samu girmamawa sosai saboda shugabancinsa, hangen nesansa, da kuma jajircewarsa ga ci gaban ƙasa.
Channels TV ta rahoto Abiodun ya jaddada jajircewar sarkin ga walwalar jama'a, yana mai ba shi yabo kan jagorantar manyan ci gaba a fannin ilimi, kiwon lafiya, da ci gaban tattalin arziki.
"A ƙarƙashin jagorancinsa, kasar Ijebu ta shaida ci gaba mai ban mamaki a fannin ababen more rayuwa da ci gaban al'umma, inda ta kafa kanta a matsayin abin koyi na ci gaba a jihar Ogun.
"Shugabancinsa bai tsaya a iya haɓaka al'adun ƙasar Ijebu ko na bikin Ojude Oba wanda ya kai matsayin duniya ba, har ma da tabbatar da ƙasar a matsayin cibiyar kasuwanci da al'adu ta ƙasa-da-ƙasa."
- Gwamna Dapo Abiodun.

Source: Twitter
Tinubu ya yi jimamin rasuwar Sarkin Ijebu
Shugaba Bola Tinubu shi ma ya yi jimamin rasuwar Awujale na Ijebuland, inda ya bayyana shi a matsayin "babban sarki na gargajiya" wanda ya yi hidima ga al'ummarsa.
A cikin wata sanarwa da aka fitar daga Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya ce ya girgiza da samun labarin rasuwar sarkin, musamman ganin cewa ta zo ne a ranar da tsohon shugaban ƙasa Buhari ya rasu.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Ganin karshe da 'yan Najeriya suka yi wa Buhari, yana tare da Atiku, El-Rufai
Ya yaba da gudunmawar sarkin ga ilimi da mulki na gari, musamman ta hanyar gudummawar da ya bayar a jami'ar Olabisi Onabanjo.
Matakan da Tinubu ya dauka bayan rasuwar Buhari
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya dauki matakai biyar na musamman bayan rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Daga cikin matakan akwai saukar da tutocin ƙasa na tsawon kwanaki bakwai da kuma tura mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, zuwa Birtaniya domin rako gawar Buhari.
Legit Hausa ta tattaro cikakkun bayanai kan waɗannan muhimman matakai da gwamnatin Tinubu ta dauka domin tunawa da Buhari da kuma girmama iyalansa.
Asali: Legit.ng

