Muhammadu Buhari: Matakai 5 da Tinubu Ya Ɗauka bayan Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa

Muhammadu Buhari: Matakai 5 da Tinubu Ya Ɗauka bayan Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa

  • Shugaba Bola Tinubu ya dauki wasu muhimman matakai biyar bayan rasuwar tsohon Shugaba Buhari, wanda ya rasu a Landan
  • Bayan rasuwar Buhari, Tinubu ya umarci a saukar da tutoci na kwana bakwai, kuma Kashim Shettima zai rako gawar daga Birtaniya
  • A wannan rahoton Legit Hausa ta yi cikakken bayani game da matakai biyar da Tinubu ya dauka don girmama marigayi Buhari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – A ranar Lahadi, 13 ga Yulin 2025, Najeriya ta shiga cikin alhini bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Legit Hausa ta ruwaito cewa Buhari ya rasu a wani asibitin London yana da shekara 82 bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Bayan rasuwar Buhari, Tinubu ya dauki muhimman matakai 5 domin karrama tsohon shugaban kasa
Shugaba Bola Tinubu ya dauki muhimman matakai 5 domin karrama Muhammadu Buhari da ya rasu. Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauki wasu manyan matakai biyar bayan rasuwar Buhari domin girmama tsohon shugaban kasar, a cewar sanarwar Bayo Onanuga a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Bidiyon kalaman Buhari na ƙarshe masu kama hankali yayin da yake barin mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya dauki matakai 5 bayan rasuwar Buhari

Marigayi Muhammadu Buhari dai ya mulki Najeriya a matsayin shugaban soja daga 1984 zuwa 1985, sannan daga baya ya sake dawowa a matsayin shugaban farar hula daga 2015 zuwa 2023.

Ga jerin matakan da Shugaba Tinubu ya bayar domin karrama marigayi Muhammadu Buhari da irin gudunmawar da ya bayar ga cigaban ƙasa da martabar Najeriya a duniya.

1. Saukar da tutoci na kwana bakwai

Shugaba Tinubu ya bayar da umarni cewa duk tutocin ƙasa a fadin Najeriya su kasance a rabin sanda daga ranar Lahadi 13 ga Yuli, zuwa tsawon kwanaki bakwai.

Wannan matakin yana nuna girmamawa da alhini na ƙasa baki ɗaya bisa rasuwar shugaban ƙasa na baya wanda ya bar tarihi mai ƙarfi a siyasa da shugabanci.

A cewar Tinubu, Buhari ya kasance shugaba mai kwazo da kyakkyawar zuciya, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ganin Najeriya ta yi fice a duniya.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ƴan Najeriya za su riƙa tuna Muhammadu Buhari da su

An aiwatar da wannan umarni a ofisoshin gwamnati, har ma da wuraren jama'a, don nuna girmamawar ƙasa ga marigayin.

2. Shettima zai rako gawar Buhari daga Birtaniya

A wani umarni na gaggawa, Shugaba Tinubu ya tura mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, zuwa Birtaniya domin rako gawar Buhari zuwa gida Najeriya.

An tsara jana'izar Buhari ne da za a yi da cikakken girmamawa a garinsa na Daura, jihar Katsina, a ranar Litinin, 14 ga Yuli, 2025, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Umarnin da Tinubu ya ba Shettima ya nuna cewa Buhari ya cancanci a dawo da shi gida da karramawa da mutunci, kasancewar ya yi shugabanci a matakai daban-daban.

Shugaban ya tabbatar da cewa wannan tafiya za ta kasance mai ingantaccen tsari domin ganin cewa an gudanar da jana'izar Buhari yadda ya dace.

3. Taron gaggawa na majalisar zartarwa (FEC)

Shugaba Tinubu ya kira zaman gaggawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) wanda aka tsara za a gudanar a ranar Talata, 15 ga watan Yuli, 2025 domin tunawa da Buhari.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ganin karshe da 'yan Najeriya suka yi wa Buhari, yana tare da Atiku, El-Rufai

Zaman zai bai wa ministoci da shugabannin ma’aikatu damar tattauna irin gudunmawar da Buhari ya bayar, tare da tunawa da ayyukansa da girmama tarihi.

Tinubu ya ce zaman zai taimaka wajen nazarin hanyoyin da gwamnati za ta gina abubuwa masu amfani don ci gaba da girmama irin gadon da Buhari ya bari.

A lokacin mulkinsa, Buhari ya fi mayar da hankali kan yaki da cin hanci da rashawa da kuma kokarin shawo kan matsalolin tsaro a ƙasa.

4. Jana'izar kasa da girmamawa ga Buhari

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnati za ta yi wa marigayi Buhari jana’izar ƙasa tare da cikakken karramawa da ya dace da matsayinsa a tarihin Najeriya.

Mun ruwaito cewa za a yi jana’izar a Daura, jihar Katsina, inda aka haife shi, kuma ana sa ran manyan shugabanni daga cikin gida da waje za su halarta don nuna girmamawa.

Gwamnatin tarayya za ta shirya komai domin tabbatar da cewa an yi wa Buhari sutura tare da birne shi cikin girmamawa, matsayin daya daga cikin shugabannin kasar.

An jaddada cewa Buhari ya rike mukamai da dama kamar gwamna, kwamishina na tarayya, soja, sannan kuma shugaban ƙasa har sau biyu.

Kara karanta wannan

Tarihi da muhimman abubuwa game da marigayi shugaba Buhari

Shugaba Tinubu ya ba da umarnin sauke tutoci na kwana 7 domin karrama Buhari da ya rasu
Shugaba Bola Tinubu tare da marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. Hoto: @officialABAT
Source: Facebook

5. Ta'aziyya ga iyalan Buhari da Katsina

Shugaba Tinubu ya kira Hajiya Aisha Buhari, matar marigayi shugaban ƙasa domin yin ta’aziyya da nuna jimami bisa wannan babban rashi da ya girgiza ƙasa.

Ya kuma miƙa sakon jaje ga dukan iyalan Buhari, gwamnatin Katsina, da kuma masarautar Daura inda Buhari ya fito, yana mai roƙon Allah ya gafarta masa.

Tinubu ya bukaci al’umma su zauna lafiya da junansu, tare da rokon Allah ya karbi rayuwarsa cikin rahama da ya azurta shi da Aljannatul Firdaus.

Shugaban ya kuma nuna cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafawa iyalan marigayin da kuma Katsina a wannan mawuyacin hali na rashi.

Naziri kan shugabancin Buhari bayan rasuwarsa

Matakan da Tinubu ya bayar za su shafe mako guda na alhini a ƙasa, inda ‘yan Najeriya ke nazari kan ayyukan Buhari da irin rawar da ya taka a tarihin ƙasar.

Mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan mulkinsa da shirye-shiryensa kamar N-Power, yaki da rashawa, da kuma kalubalen da suka shafi tattalin arziki da tsaro.

Kara karanta wannan

Rasuwar Buhari: Tinubu ya tura Shettima ya ɗauko gawar tsohon shugaban kasa a London

Duk da wasu sun nuna rashin jin daɗi da wasu bangarorin mulkinsa, Tinubu ya ce ya kamata a hada kai domin a girmama wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga kasar.

Yayin da kasar ke shirin jana’izar tsohon shugaban kasa, wadannan matakai da Tinubu ya dauka sun nuna yadda gwamnati ke daraja Buhari da irin gudunmawar da ya bayar.

Ganin karshe da aka yi wa Buhari

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Atiku Abubakar da wasu manyan 'yan siyasa a ranar 11 ga Afrilun 2025.

Bidiyon ganawarsu ya karade intanet, inda aka ga tsohon shugaban cikin nishadi, wanda hakan shi ne ganinsa na karshe kafin rasuwarsa a ranar 13 ga Yulin 2025.

Daga lokacin aka ce ba a sake ganin wani bidiyon Buhari ba, sai a ranar Lahadi kwatsam, Garba Shehu ya sanar da rasuwar Buhari a London.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com