Bidiyon Kalaman Buhari na Ƙarshe Masu Kama Hankali yayin da Yake Barin Mulki
- An gano bidiyon karshe da Muhammadu Buhari yana magana kafin barin mulki, inda ya roki gafarar 'yan Najeriya bisa kura-kuran mulkinsa
- Buhari ya ce ya san ya bata wa mutane da dama rai ta hanyoyi daban-daban, kuma yana fatan za su yafe masa har zuciya
- Ya bukaci duk wanda yake ganin an yi masa rashin adalci ko cin rai da ya yafe, yana mai cewa mu duka 'yan Adam ne
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - An tabbatar da mutuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a yammacin yau Lahadi 13 ga watan Yulin 2025.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Garba Shehu shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya a yammacin yau Lahadi.

Source: Twitter
An gano wani faifan bidiyo da @Kawu Garba ya wallafa a X wanda shi ne kalaman Buhari na karshe yayin barin mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari: Yadda Tinubu ya aika Shettima zuwa London
Sanar da rasuwar Buhari ke da wuya, fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa ta musamman tare da tura sakon ta'aziyya ga dukan yan Najeriya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da rasuwar Muhammadu Buhari a London da misalin ƙarfe 4:30 na yamma bayan rashin lafiya.
Tinubu ya tattauna da Aisha Buhari don jajanta mata sannan ya umarci Kashim Shettima da ya rako gawar marigayin shugaban ƙasar.
Buhari ya taɓa mulki a matsayin shugaban soja da na farar hula, yayin da Tinubu ya umurta da a sauke tutoci domin girmama marigayin.

Source: Twitter
Bidiyon Buhari yana neman afuwar ƴan Najeriya
A cikin bidiyo, Buhari ya tabbatar da cewa ya sani akwai mutane da dama da ya bata musu rai.
Buhari ya nemi yafiyar yan Najeriya da dama wadanda ya bata musu ta kowace hanya wanda ba zai taba sani ba.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Ganin karshe da 'yan Najeriya suka yi wa Buhari, yana tare da Atiku, El-Rufai
A cikin bidiyon, Buhari ya ce:
“Duk wanda yake ganin an yi masa wani rashin adalci, mu duka ‘yan Adam ne.
"Babu shakka na bata wasu rai, kuma ina fatan za su yafe mini.
"Kuma ga wadanda suke ganin na bata musu rai sosai, don Allah ku yafe mini.”
Martanin yan Najeriya bayan mutuwar Buhari
Mutuwar Buhari ta jawo martanin miliyoyin mutane da dama daga dukan bangarorin kasar Najeriya baki daya.
Mafi yawan mutane sun yi ta masa addu'ar samun rahama da fatan Ubangiji ya karbi bakuncinsa.
Har ila yau, akwai wadanda bayan tabbatar da mutuwarsa sun yi alkawari tare da yafe masa dukan abin da ya yi musu a matsayinsa na wanda ya shugabance su.
Legit Hausa ta yi magana da wasu
Muhammad Salisu Adamu ya ce shi ya dade da yafewa Buhari tun ma kafin Allah ya dauki ransa a yau Lahadi.
Khamis Muhammad a Gombe ya ce a gaskiya yau ya ji ba dadi bayan samun labarin rasuwar tsohon shugaban kasa.
Ya ce:
"A yau na yanke shawarar yafe masa, amma ko a jiya ina jin ba zan taba yafe masa ba, amma komai ya wuce Allah ya yi masa rahama.
Bidiyon Buhari da Atiku kafin tafiya London
Kun ji cewa a ranar 11 ga Afrilun 2025, Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan siyasa sun kai ziyara gaisuwar Sallah ga Muhammadu Buhari a Kaduna.
Bidiyon ganawarsu ya karade intanet, inda aka ga tsohon shugaban cikin nishadi, wanda hakan shi ne ganinsa na karshe kafin rasuwarsa.
Daga lokacin aka ce ba a sake ganin wani bidiyon Buhari ba, sai a yau Lahadi kwatsam, Garba Shehu ya sanar da rasuwar Buhari a London.
Asali: Legit.ng

