Abubuwan da Ƴan Najeriya Za Su Riƙa Tuna Muhammadu Buhari da Su
FCT, Abuja - A yammacin yau aka tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a Birtaniya.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya shafe wani lokaci yana jinya a birnin London bayan ya sauka a mulki shekaru biyu da suka wuce.

Source: Twitter
An tabbatar da mutuwar Buhari a London
Tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Garba Shehu shi ya tabbatar da haka a yammacin yau Lahadi 13 ga watan Yulin 2025 a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutuwar Muhammadu Buhari ta girgiza Najeriya baki daya wanda al'umma suke yi masa fatan samun rahama.
Buhari ya mulki Najeriya daga ranar 29 watan Mayun shekarar 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023.
Bayan saukarsa, Bola Tinubu ya karbi ragamar mulki bayan lashe zaben da aka gudanar a 2023.

Source: Facebook
Tsammanin yan Najeriya kan mulkin Buhari
Sai dai akwai wasu abubuwa da dama da suka faru a lokacin mulkin Buhari da yan Najeriya ba za su mantaba.
Kafin bawan Buhari mulki, yan Najeriya musamman daga Arewacin Najeriya suna tsammanin samun shugabanci nagari.
Sai dai an samu akasin haka bayan darewarsa mulki inda abubuwa suka sake tabarbarewa.
Legit Hausa ta yi duba kan wasu abubuwa da suka faru a mulkin da ba za a manta da su ba.
1. Abubuwan da aka tsammata lokacin Buhari
* Yaƙi da cin hanci da rashawa
Buhari ya shahara a matsayin mutumin kirki marar son duniya, saboda salon rayuwarsa da kuma kwarewarsa ta soja.
'Yan Najeriya sun yi fatan zai kama manyan barayin gwamnati da kwato kudaden da aka wawure.
An kuma sa rai zai kawo gaskiya da adalci a mulki tare da mutunta doka da oda a matsayinsa na kwararren soja.

Source: Twitter
* Tsaro da Boko Haram

Kara karanta wannan
Bidiyo: Ganin karshe da 'yan Najeriya suka yi wa Buhari, yana tare da Atiku, El-Rufai
Tun da soja ne, mutane da dama musamman a Arewa maso Gabas sun yi imanin zai murƙushe Boko Haram.
An yi fatan dawowar zaman lafiya da komawar ‘yan gudun hijira zuwa garuruwansu da rashin tsaro ya daidaita.
* Tattalin arziki da ayyuka
Buhari ya yi alkawarin sauya hanyoyin samun kudin shiga daga mai zuwa noma da ma’adinai.
Ya kuma yi alkawarin samar da miliyoyin ayyuka da gina manyan ababen more rayuwa kamar aikin wutar lantarkin Mambilla.
Mutane sun sa rai Buhari zai daidaita darajar naira, rage hauhawar farashi da ƙarfafa kwarin gwiwar masu zuba jari.
2. Abin da gaskiya ta nuna lokacin mulkinsa
* Tattalin arziki/hauhawar farashi
* Rugujewar tattalin arziki: Najeriya ta shiga matsala game da tattalin arziki a shekarar 2016 da 2020 sakamakon sauyin farashin danyen mai da raunin matakan gwamnati.
* Hauhawar Farashi: Tun daga 9% a 2015, hauhawar farashi ta ci gaba da tashi har ta kai fiye da 20% a 2022, farashin abinci ya zama bala’i.
* Faduwar Naira: Naira ta faɗi daga ₦197/$1 a 2015 zuwa kusan ₦460/$1 a kasuwa na hukuma da sama da ₦700/$1 a kasuwar bayan fage a 2023.
* Badakalar Godwin Emefiele
Gwamnan Babban Banki,'n Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, ya aiwatar da manufofi marasa tabbas da dama kamar tsarin "Naira kan Dala", Channels TV ta ruwaito.
An zarge shi da buga tiriliyan na Naira don ɗora wa gwamnati nauyi wanda ake ganin ya jawo matsaloli da dama.
A ƙarshe, a 2023 hukumar DSS ta kama shi a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, inda aka gano yawan barna da ake zargi da yi a CBN.

Source: Facebook
* Sake fasalin Naira (2022–2023)
An ce manufar sauya fasalin Naira na ƙarshen mulkinsa an yi ne don hana sayen ƙuri’u da rage ajiya, TheCable ta ruwaito.
Amma gazawar aiwatarwa ta jawo rashin kudi, layi a bankuna, da tabarbarewar kasuwanci wanda ya jawo matsin tattalin arziki.
Abubuwan da suka ɓatawa Buhari suna a Arewa
* Aikin wutar lantarkin Mambilla
An yi alkawarin aikin wutar lantarki mai karfin 3,050 MW, amma bai wuce kawai a takarda ba cikin shekaru takwas, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Rasuwar Buhari: Tinubu ya tura Shettima ya ɗauko gawar tsohon shugaban kasa a London
Rigima da kwangiloli da ƙarancin kudade da rashin jajircewa sun hana ci gaba, ya zama abin misali ga alkawura da ba a cika ba.
* Aikin hakar man fetur na Kolmani
Buhari ya kaddamar da aikin man Kolmani a Bauchi/Gombe a 2022 a matsayin jigon arzikin Arewa, cewar rahoton Nairametrics.
Sai dai zuwa 2023 ba a fara hakar mai da gaske ba, yayin da masu sukar gwamnati sun ce aikin ya fi zama gagarabadau na siyasa da aka yi ba tare da cikakken bayani ba.

Source: Twitter
* Kage kan "Jubril na Sudan"
A 2017–2018, jita-jita suka yadu cewa Buhari ya mutu a London kuma wani dan Sudan mai suna Jubril aka maye gurbinsa.
Ko da ba gaskiya ba ce, jita-jitar ta karbu saboda rashin bayani da ɓoye bayanan lafiyarsa, cewar rahoton Punch.
Buhari ya musanta hakan daga bisani, amma hakan ya nuna yadda mutane ke rasa aminci da shugabanci a wancan lokaci.
Buhari ya nemi afuwa a bidiyonsa na ƙarshe
Kun ji cewa an yada wani bidiyon karshe da Muhammadu Buhari yake magana kafin barin mulki, inda ya roki gafarar 'yan Najeriya bisa kura-kuran mulkinsa.

Kara karanta wannan
'An yi babban rashi': Tsohon shugaban kasa Buhari ya rasu, ƴan Najeriya sun magantu
Buhari ya ce ya san ya bata wa mutane da dama rai ta hanyoyi dabam-dabam, kuma yana fatan za su yafe masa daga zuciya.
Ya bukaci duk wanda yake ganin an yi masa rashin adalci ko cin rai da ya yafe, yana mai cewa mu duka 'yan Adam ne.
Asali: Legit.ng

