Rasuwar Buhari: Tinubu Ya Tura Shettima Ya Ɗauko Gawar Tsohon Shugaban Kasa a London
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da rasuwar Muhammadu Buhari a Landan da misalin ƙarfe 4:30 na yamma bayan rashin lafiya
- Tinubu ya tattauna da Aisha Buhari don jajanta mata sannan ya umarci Kashim Shettima da ya rako gawar marigayin shugaban ƙasar
- Buhari ya taɓa mulki a matsayin shugaban soja da na farar hula, yayin da Tinubu ya umurta da a sauke tutoci domin girmama marigayin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da rasuwar magabacinsa, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Buhari ya rasu ne a Landan da misalin karfe 4:30 na yammacin Lahadi, bayan doguwar jinya.

Source: Facebook
An tura Shettima ya rako gawar Buhari
Mai magana da yawun Tinubu, Bayo Onanuga ne ya fitar da wannan sanarwar a shafinsa na X a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya riga ya yi magana da Hajiya Aishat Buhari, matar tsohon shugaban ƙasa, inda ya jajanta mata sosai kan wannan babban rashi.
Bugu da ƙari, Shugaba Tinubu ya bayar da umarni ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da ya tafi kasar Ingila domin ya rako gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa Najeriya.
Buhari: An ba da umarnin sauke tuta
Sanarwar ta ce marigayi tsohon shugaban kasa Buhari ya zama shugaban Najeriya bayan da aka zaɓe shi sau biyu, a shekarar 2015 da kuma 2019.
Ya kuma taɓa zama shugaban kasa na soja tsakanin watan Janairun 1984 zuwa watan Agustan 1985.
A matsayin alamar girmamawa ga shugaban da ya rasu, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a saukar da tutocin ƙasa zuwa rabin sanda a duk faɗin ƙasar.

Source: Facebook
Martanin 'yan Najeriya kan rasuwar Buhari
Legit Hausa ta tattaro martanin 'yan Najeriya kan rasuwar Buhari:

Kara karanta wannan
'An yi babban rashi': Tsohon shugaban kasa Buhari ya rasu, ƴan Najeriya sun magantu
@abdullahayofel:
"Allah ya gafarta wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kuma sa ya huta a Aljanna Firdaus."
@DrKalu_PhD:
"NNa yi farin ciki kwarai. Ba za ka lalata ƙasa ba kuma ka rayu lafiya!"
@mrbrightgil:
"Me ya sa za a ce Tinubu ya ‘ba da umarni’ ga Kashim Shettima? Ba za ku iya amfani da kalma mafi kyau ba? Dole sai kun raina mataimakin shugaban kasa… Umurni fa?"
@AkileIjebu_GCON:
"Allah ya jikansa. Najeriya ta rasa mutum mai gaskiya, dan kasa nagari, soja a fagen yaki, dan dimokuradiyya a siyasa, shugaba mai tsoron Allah, kuma uba nagari ga iyalansa. Ina mika ta’aziyyata ga iyalinsa da kuma Shugaba Tinubu.
@ObasaOluwadami2:
"Ya kamata shugaban kasa ya ayyana hutun kasa domin mu yi makoki kan rasuwar tsohon shugaban kasa."
@h_okueso1111:
"Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma saka masa da Aljanna Firdaus. Aameen."
@ojoteosas:
"Lafiya lau Buhari, yanzu Tinubu, Wike da Akpabio su sani babu abin da ke dawwama. Buhari da yake tamkar ginshiki shekaru kalilan da suka wuce, ya riga mu. Haka ma sauran shugabannin da ke zaluntar al’umma za su bi sahunsa."
A zantawarsa da Legit Hausa, Al'Ameen Muhammad ya nuna matukar kaduwarsa bisa rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Al'Ameen Muhammadu ya ce:
"Na girgiza matuka da na ji cewa Buhari ya rasu. Wannan ne karo na biyu da shugaban kasa ko tsohon shugaban kasa ya rasu da na girgiza, na farkon shi ne Umaru Musa Yar'Adua.
"Muna addu'ar Allah ya jikansa, ya gafarta masa kura kuransa, ya kuma ba iyalansa hakurin jure wannan rashi da aka yi."
Shi kuwa Al'Yasa'u Sulaiman cewa ya yi:
"Ba za mu manta da irin ayyukan da Buhari ya kawo mana ba. Gwamnatinsa ta yi duk wani kokari na inganta matasa, kama da rancen kudi na Ancho Borrowers, tallafin N-Power da sauransu.
"Hakika Buhari ya so yin mulkin Najeriya, kuma Allah ya ba shi, kuma ya gama lami lafiya. A karshe mai afkuwa ta afku a kansa. Allah ya jikansa."
Tsohon Shugaba Buhari ya rasu a London
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rasu a asibitin da yake jinya a London bayan ya fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan
Garba Shehu ya fadi halin da Buhari yake ciki bayan kwantar da shi a asibitin Landan
Tsohon mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu ne ya sanar da cewa Buhari ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yulin 2023.
'Yan Najeriya sun nuna kaduwarsu da suka samu labarin rasuwar tsohon shugaban kasar. Da yawa sun yi addu'ar Allah ya jikan Buhari ya ba iyalansa hakurin rashin.
Asali: Legit.ng

