Dalilin da Ya Sa Majalisa Ta Ki Dawo da Sanata Natasha duk da Umarnin Kotu
- Majalisar dattawan Najeriya ta yi magana kan dalilin da ya sa ba ta dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bakin aiki ba
- Kakakin majalisar, Yemi Adaramodu ya bayyana cewa suna jiran kwafin hukuncin kotun ne wanda ya umarci a dawo da ita
- Ya bayyana cewa har sai sun samu kwafin hukuncin, sun duba shi sannan za su ɗauki matsaya a kan batun
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta bayyana dalilin da ya sa ba za ta bari Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dawo bakin aikinta ba.
Majalisar dattawan ta ce ba za ta dawo da Natasha ba har sai ta duba abin da ke kunshe a cikin kwafin hukuncin kotu (CTC), dangane da shari’ar da ta shafi tsakaninta da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Source: Facebook
Daily Trust ta ce shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yaɗa labarai, Sanata Yemi Adaramodu, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a birnin Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta dakatar da Sanata Natasha
Majalisar dattawa dai ta dakatar da Natasha Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga watan Maris na tsawon watanni shida, a lokacin da take tsaka da zargin shugaban majalisar, Godswill Akpabio, da cin zarafinta.
An dakatar da ita ne bayan da kwamitin majalisar dattawa kan ƙa’idoji da karɓar ƙorafe-ƙorafe ya bayar da shawarar hakan, kamar yadda shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen (APC-Edo ta Kudu Kudu) ya gabatar.
A cikin matakan dakatarwar, an dakatar da biya mata albashi, an cire mata jami’an tsaro, kuma an hana ta shiga harabar majalisar dokoki ta ƙasa gaba ɗaya.
Daga bisani, Sanata Natasha ta kai ƙarar wannan hukunci a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda mai Shari’a Binta Nyako ta bayar da umarnin cewa a dawo da ita bakin aiki.
Sai dai kotun ta hukunta Akpoti-Uduaghan bisa cin mutuncin kotu tare da umartar ta biya tara ta N5m.

Kara karanta wannan
Duk da hukuncin kotu, Sanata Natasha ta rasa babban mukaminta a majalisar dattawa

Source: Facebook
Meyasa majalisa ta ƙi dawo da Natasha?
Yemi Adaramodu, wanda shi ne kakakin majalisar dattawa, ya ce majalisar ta riga ta nemi kwafin CTC tun daga ranar Litinin, yana mai jaddada cewa har sai an karɓi takardun an duba su, sannan za a ɗauki matsaya, rahoton Punch y tabbatar.
"Majalisar dattawa ta nemi CTC tun ranar Litinin. Muna sa ran karɓar takardun, kuma da zarar mun karɓa, za mu yi biyayya ga abin da ke cikin hukuncin kotun."
"Amma da farko, majalisa za ta zauna ta tattauna kan abin da ke cikin CTC, kuma idan mun duba abubuwan da ke ciki, sai mu ɗauki matsaya."
- Sanata Yemi Adaramodu
Majalisa ta ƙwace muƙamin Sanata Natasha
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta ƙwace muƙamin shugabanci da ta ba Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Majalisar ta ƙwace muƙamin shugabancin kwamitin harkokin ƴan gudun hijira da sa-kai daga hannun Sanata Natasha.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya naɗa sabon sanata wanda zai maye gurbin Natasha a muƙamin.
Asali: Legit.ng
