'Malamai ne Matsalarmu Wallahi': Sheikh Ya Soki Jingir, Ya ba Sambo Rigachukun Shawara

'Malamai ne Matsalarmu Wallahi': Sheikh Ya Soki Jingir, Ya ba Sambo Rigachukun Shawara

  • Sheikh Muhammad Nuru Khalid ya nuna damuwa da kalaman Sheikh Sani Jingir game da Malam Yusuf Sambo Rigachukun
  • Sheikh ya ce malamai su ne matsalar Najeriya, idan aka gyara su komai zai daidaita, ya bukaci a daina jifan juna da kalmomin batanci
  • Ya ce zargin Peter Obi da kisan Sardauna ba daidai ba ne, ya roki malamai da mabiyansu su guji tayar da fitina a kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Malam Muhammad Nuru Khalid ya yi tsokaci kan maganganun Sheikh Sani Yahaya Jingir.

Shehin malamin ya nuna damuwa kan yadda Jingir ya caccaki Malam Yusuf Sambo Rigachukun bayan tarbar Peter Obi.

Sheikh ya caccaki Jingir kan kalamansa da ya yi
Sheikh Nuru Khalid ya soki Jingir game da Sambo Rigachukun. Hoto: Sheikh Muhammad Nuru Khalid, Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun.
Source: Facebook

Sheikh Nuru Khalid ya soki malaman Musulunci

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Asabar 12 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Bayan katoɓarar Wike, Coci ya ɗauki mataki, ya hana ƴan siyasa hawa mimbari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, malamin ya ce babbar matsalar Najeriya malaman Musulunci ne suke jawowa.

"Matsalar kasar nan wallahi malamai ne, malamanmu na Musulunci su ne matsalar Najeriya.
"Idan ka seta su, Najeriya za ta setu ina kira ga malamai masu daraja, iyayenmu bai kamata suna amfani da wasu kalmomi ga juna ba.
"Malam Yusuf Sambo, malamin addini ne yana da daraja a cikin al'umma, Sheikh Sani Yahaya Jingir malamin addini ne yana da daraja a Musulunci.
"Amma wallahi idan aka ce daya daga cikinsu zai na cewa daya mahaukaci a kafofin sadarwa, to al'ummarmu ta gama.
Kalaman Jingr game da Obi sun jawo maganganu
An caccaki Sheikh Jingir kan kalamansa game da Peter Obi. Hoto: JIBWIS Gombe State.
Source: Facebook

Sheikh ya gargadi Jingir kan zargin Obi

Sheikh Nuru Khalid ya bayyana rashin jin dadi kan abin da ke faruwa inda ya ce ta yaya za a gyara al'umma a haka.

Malamin ya bayyana girman zargin da Sani Yahaya Jingir ya yi kan Peter Obi game da kisan kai da cewa babban lamari ne.

Kara karanta wannan

'Allah ya kashe su': Sheikh ya yi addu'o'i ga azzaluman shugabanni a gaban Peter Obi

Ya kara da cewa:

"Da irin wannan ne za ku saita mu? Da irin wannan za ku kai Musulmai ga nasara? Ace kamar malami Sani Yahaya Jingir bai san girman zargin mutum da kisa ba.
"Ka zargi Peter Obi da cewa shi ya kashe Sardauna, za ka jawo mana bala'i a kasar nan.
"Wallahi wadanda suke kusa da Malam Sani Yahaya Jingir su fada masa gaskiya ka da ya jawo mana bala'i a Najeriya.

Shawarar da Sheikh ya ba Sambo Rigachukun

A karshe, Malam ya shawarci Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun da mabiyansa da su yi hakuri.

A cewarsa:

"Muna ba Malam Yusuf Sambo hakuri don Allah ya dauki dattaku ka da ya mayar da martani, ka da wani mabiyinsa ya mayar da martani.
"Su kuma yan soshiyal midiya don Allah ka da su rika habaka irin wadannan zantuttuka a cikin al'umma, Allah ya sa mun dace."

Jingir ya caccaki Rigachukun kan Peter Obi

Kara karanta wannan

Peter Obi: Siyasa za ta rikita Izala, Jingir ya yi wa Yusuf Sambo zazzafan raddi

Kun ji cewa shugaban malaman Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi kakkausar suka kan Sheikh Yusuf Sambo bayan ya karɓi Peter Obi a Kaduna.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da maganar siyasa da yunkurowar 'yan adawa da suke kalubalantar Bola Tinubu.

Maganganun Sheikh Jingir sun tayar da kura a kafafen sada zumunta, inda wasu ke kwatanta su da irin tarbar da ya taba yi wa Rochas Okorocha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.