An Maka Sanusi II a Kotu bayan 'Umarnin' Korar Masoyan Aminu Ado daga Fadarsa

An Maka Sanusi II a Kotu bayan 'Umarnin' Korar Masoyan Aminu Ado daga Fadarsa

  • Wasu manyan ma’aikatan fada tara sun shigar da kara a kotu kan korarsu daga gidan fadar Sarki Sanusi II
  • Usman Sallama Dako ya ce an rusa gidansa ne saboda goyon bayansa ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero
  • Kotun ta umurci a dakata da duk wani abu, tana kuma ba da izinin isar da sammaci ta ofishin majalisar masarauta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Korar wasu masoyan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya sake daukar sabon salo a jihar bayan shigar da kara kotu.

Wasu manyan ma’aikatan fada tara sun shigar da kara a kan Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II.

An shigar da korafi a kotu kan Sanusi II
An shigar da Kara a kotu bayan korar masoyan Aminu Ado daga fada. Hoto: Sanusi Bature D/Tofa.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da suka sanyawa hannu wanda shafin Nasara Radio ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Kotu ta raba gardama kan karar da Abba Hikima ya shigar da Wike a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Sallama ya ce kan korarsu a fada

A cikin wani bidiyo da Legit Hausa ta samu, Dako ya bayyana cewa wasu jami’an fada sun gaya masa cewa sarkin yana so ya kora duk masu goyon bayan Bayero.

Ya ce:

“Ina waje ne lokacin da matata ta kira ta ce wasu bata-gari suna rusa gidan, da na dawo, na iske gidan cikin matsanancin hali

Ya kuma bayyana cewa gidan na mahaifinsa ne, wanda marigayi Sarki Ado Bayero ya ba shi.

“Mahaifina an haife shi a cikin fada, ni ma haka. Don haka ban ga dalilin korar mu ba saboda muna goyon bayan Aminu, alhali mahaifinsa ya nuna mana karamci."

- Cewar Dako

Duk da an kore shi, Dako ya jaddada biyayyarsa ga Aminu Ado Bayero wanda ya ce shi ne ya mayar da su mutane.

Korar masoyan Aminu Ado a fada ya sake sauya salo
An kai karar Sanusi II a kotu bayan korar masoyan Aminu Ado daga fada. Hoto: Sanusi II Dynasty, Masarautar Kano.
Source: Twitter

Dalilin maka Sanusi II a kotun Kano

Daga cikinsu, mutane 12 da abin ya shafa suna zargin korar su ba bisa ka’ida ba da rushe gidajensu da ke cikin fadar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta karbo bashin Dala miliyan 747 domin aikin titi a Legas

An shigar da karar mai lamba K/M1607/2025 a gaban Mai Shari’a Musa Ahmad na sashen shari’a na Bichi a Kano.

Masu karar, wadanda Usman Dako, Galadiman Sallama ke jagoranta, sun hada da masu rike da mukaman fada da kuma wasu ma’aikata.

Sun zargi sarkin da majalisar masarautar Kano da cewa suna hukunta su ne saboda biyayya ga Sarkin da aka sauke, Aminu Ado Bayero.

Sauran wadanda ake karar sun hada da Sufeto Janar na ‘yan sanda, DSS, NSCDC da wasu jami’an fada.

Umarnin da kotun da bayar a Kano

Kotun ta bayar da umarnin cewa dukkan bangarorin su ci gaba da zama kamar yadda suke kafin rigimar, cewar rahoton Leadership.

Haka kuma, ta bayar da izinin mika takardun kotu ta hanyar ofishin majalisar masarauta da kuma hanyar sako ga wadanda ke zaune a Abuja.

Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ko majalisar masarautar Kano ba su fitar da sanarwa kan lamarin ba.

An soki Sanusi kan korar masoyan Aminu Ado

Kara karanta wannan

Wike ya bayar da umarni kan mabarata da masu sana’o’i da suka cika titunan Abuja

A wani labarin, ana zargin Sarki Sanusi II da bayar da umarnin korar wasu masoyan Aminu Ado Bayero daga fadar Sarki saboda rashin biyayya.

A wani bidiyo, Sani Kwano ya bayyana cewa mahaifiyarsa ta taimaki Sanusi II fiye da yadda danginsa suka taba kula da shi.

Kwano ya ce su fiye da mutum 200 ne a gidan Sarki, kuma ba duka suke adawa da Sanusi ba, wasu suna tare da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.