NiMet: Za a Sha Ruwa da Tsawa a Kano, Yobe da Jihohin Arewa 13 a ranar Lahadi
- Hukumar NiMet ta fitar da hasashen cewa za a samu ruwan sama da tsawa a yawancin sassan Najeriya a ranar Lahadi, 13 ga Yuli
- Jihohin da ke Arewa kamar Kano, Bauchi, Yobe, da Nasarawa za su fuskanci tsawa da ruwan sama mai ƙarfi daga safiya zuwa dare
- NiMet ta gargaɗi ‘yan Najeriya da su ɗauki matakan kariya daga haɗarin ambaliya, iska mai ƙarfi, da kuma katsewar lantarki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Hukumar NiMet ta fitar da hasashen yanayi na yau Lahadi, 13 ga Yulin 2025, inda ta ce za a iya samun ruwa da tsawa a mafi yawan sassan ƙasar.
Hukumar ta buƙaci jama'a da su kasance cikin shiri don fuskantar haɗarin ambaliyar ruwa, iska mai ƙarfi, da kuma katsewar ayyukan sadarwa ko lantarki.

Source: Getty Images
Sanarwar yanayin, wacce NiMet ta fitar a ranar 12 ga Yulin 2025 a shafinta na X, ta bayyana cikakken yanayin da ake sa ran za a samu a jihohin Arewa da Kudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana sa ran ruwa da tsawa a Arewa
A safiyar yau Lahadi, NiMet ta bayyana cewa ana sa ran za a samu tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Yobe, Kano, Jigawa, da Bauchi.
Ana kuma sa ran tsawa tare da ruwan sama mai ƙarfi a sassan jihohin Adamawa, Taraba, Zamfara, Kebbi, Bauchi, Borno, Jigawa, da Yobe daga yamma ruwa dare.
Har ila yau, ana sa ran hadari tare da walkiya za su mamaye faɗin yankin a safiyar Lahadi a yankin Arewa ta Tsakiya.
Da yamma zuwa dare kuwa, ana sa ran tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Plateau, Nasarawa, Kogi, Benue, da Niger.
Hasashen ruwan sama a Kudancin Najeriya
A safiyar yau Lahadi a jihohin Kudu, ana sa ran hadari zai hadu tare da yiwuwar ɗan ruwan sama a jihohin Anambra, Abia, Ebonyi, Imo, Bayelsa, Delta, Cross River, Akwa Ibom, da Rivers.
Ana sa ran za a ci gaba da samun ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a yawancin sassan yankin kudancin Najeriya daga yamma zuwa dare.

Source: Original
Gargadi ga jama'a kan hatsarin ruwa da iska
NiMet ta shawarci jama'a da su ci gaba da kasancewa cikin shiri don fuskantar haɗarin ambaliyar ruwa ta farat ɗaya, iska mai ƙarfi, da kuma katsewar ayyuka na gida sakamakon tsawa da ruwan sama.
Hukumar ta kuma shawarci direbobi da su guji tuki a cikin ruwan sama mai ƙarfi don kauce wa haɗurruka.
Haka kuma, an yi gargaɗi da a guji fakewa a ƙarƙashin bishiyoyi yayin ruwan sama saboda haɗarin faɗuwar rassa.
An bukaci kamfanonin jiragen sama su samu rahotannin yanayi na filayen jiragen sama da kuma bayanan jirage daga NiMet don tabbatar da tafiye-tafiye lafiya.
Jihohin da za su fuskanci ambaliyar ruwa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnati ta bayyana yiwuwar ambaliya a garuruwa 1,249 a kananan hukumomi 176 da ke cikin jihohi 30 da Abuja.
Ministan albarkatun ruwa, Farfesa Joseph Utsev, ya ce sauyin yanayi na kara haddasa ambaliya, wanda zai shafi sana'o'i, muhalli da zirga-zirga.
Rahoton NIHSA na 2025 ya lissafa jihohi 30 da ambaliyar ruwan za ta shafa da suka hada da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra da Bauchi.
Asali: Legit.ng


