An Buƙaci a Raba Kano zuwa Jihohi 2 da Ƙirƙiro Sababbin Kananan Hukumomi 26
- Kano ta buƙaci a raba ta zuwa jihohi biyu tare da kirkiro ƙarin ƙananan hukumomi 26 daga cikin 44 da ake da su a yanzu
- Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo ne ya miƙa wannan buƙata a taron sauraron ra'ayin jama'a kan kudirin gyara kundin tsarin mulki
- Gwamnatin Kano ta ce jihar tana da ɗumbin al'umma da faɗin ƙasa, don haka akwai buƙatar ƙara jiha da kananan hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnatin Kano ta bukaci a ƙirƙiri sabuwar jiha daga cikin iyakokinta na yanzu tare da ƙarin ƙananan hukumomi guda 26 a jihar.
Gwamnatin ta miƙa wannan buƙata ne a wani ɓangare na shawarwarin da ta gabatar wa Kwamitin Majalisar Wakilai na gyaran kundin tsarin mulki.

Source: Original
Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Gwarzo, ne ya gabatar da wannan buƙata yayin taron jin ra'ayin jama'a na yankin Arewa maso Yamma da aka yi a Kaduna, Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin ƙara sababbin ƙananan hukumomi a Kano
A taron wanda ya gudana yau Asabar, Aminu Gwarzo ya ce ƙara ƙananan hukumomi 26 daga 44 da ke Kano ya zama dole sakamakon yawan al’umma da faɗin ƙasa da jihar ke da su.
A cewarsa, hakan zai ƙara kusantar da gwamnati ga al'umma domin sauƙaƙa ci gaba da warware matsalolin da jama'a ke fuskanta, rahoton Tribune Online.
Gwarzo ya jaddada cewa duba da girman jihar da yawan al'ummarta, lokaci ya yi da za a ƙirƙiro sabuwar jiha daga cikin Kano, sannan a ƙara yawan ƙananan hukumomi daga 44 zuwa 70.
Kano ta goyi bayan ƙirƙiro jihohi a Najeriya
“Kano na goyon bayan kiraye-kirayen da ake yi na sake fasalin tsarin mulki, kuma muna maraba da ƙirƙirar sababbin jihohi matuƙar hakan ya cika sharuddan da ke Sashe na 8 na Kundin Tsarin Mulki.
"Haka kuma muna da cikakken goyon baya ga ƙirƙirar ƙananan hukumomi 26 a Kano domin cika burin al’ummar mu."

Kara karanta wannan
Kudirin ƙirƙiro karin jiha 1 a Arewacin Najeriya ya samu gagarumin goyon baya a Majalisa
- Aminu Gwarzo.
Wannan bukata na kunshe ne a cikin takardar da Gwamna Abba Kabir Yusuf da al’ummar Kano suka amince da ita bayan doguwar tattaunawa da neman ra’ayoyin jama’a.

Source: Facebook
Kano ta buƙaci sakar wa kananan hukumomi mara
Baya ga buƙatar ƙarin ƙananan hukumomi da jiha, Kano ta kuma nemi a bayyana a fili a kundin tsarin mulki cewa ƙananan hukumomi su ne mataki na uku na gwamnati.
Jihar ta ba da shawarar sauya sashe na 2(2), sashe na 7 da sashe na 162(5) domin sakar wa ƙananan hukumomi mara su ci gashin kansu.
"Kano ta lura da yadda ake kallon ƙananan hukumomi a matsayin wani ɓangare da ba shi da muhimmanci . Muna neman sauye-sauye da za su ba su cikakken ƴanci a kundin tsarin mulki," in ji Gwarzo.
Gwamna Abba ya naɗa shugaban ma'aikatansa
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗa Dr. Suleiman Wali Sani a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano.
A watan Disamba, 2024 Gwamna Abba ya rufe ofishin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Kano bayan tsige Shehu Wada Sagagi.
Gwamna Abba ya ce ya yanke shawarar dawo da ofishin shugaban ma'aikatan ne domin ƙarfafa harkokin shugabanci da yi wa al'umma aiki.
Asali: Legit.ng

