Adamawa: Gwamna Fintiri Ya Ƙaƙaba Dokar Hana Fita bayan Ɓarkewar Rikici

Adamawa: Gwamna Fintiri Ya Ƙaƙaba Dokar Hana Fita bayan Ɓarkewar Rikici

  • Gwamna Ahmadu Fintiri ya sanya dokar hana fita daga safiya zuwa dare a wata karamar hukumar a jihar Adamawa
  • Hakan ya biyo bayan barkewar rikici tsakanin kabilu biyu wanda ya jawo asarar dukiyoyi a jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Rikicin tsakanin al’ummomin Chibo da Bachama ya kai kololuwa bayan kona gidaje 36, wanda ya samo asali daga gardamar fili tun shekaru da suka wuce

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya dauki mataki bayan cigaba da barkewar rikici a jihar.

Gwamna Fintiri ya sanya dokar hana fita daga safiya zuwa dare a karamar hukumar Lamurde saboda rikicin kabilanci.

An sanya dokar hana fita a Adamawa
Gwamna Fintiri ya sanya dokar hana fita a Adamawa. Hoto: Gov. Ahmadu Umaru Fintiri.
Source: Facebook

Adamawa: Gwamna Fintiri ta sanya dokar hana fita

Premium Times ta ce dokar ta fara aiki nan take domin dawo da doka da oda a jihar da ke Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Harin ƴan bindiga: Mutane sun ji azaba, sun fara tserewa daga gidajensu a Filato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan rikici tsakanin kabilun Chibo da Bachama da ake yi da juna har na tsawon kwanaki.

Rikicin ya fi tsananta a farkon makon nan, inda rundunar ‘yan sanda ta bayyana konewar bukkokin zama 33 da wasu manyan gidaje guda uku.

Rundunar ‘yan sanda ta danganta rikicin da wani dogon rikici na filaye wanda kotu ta kasa warwarewa tsawon shekaru.

Gwamna ya sanya dokar hana fita a Adamawa
Gwamna Fintiri ya saka dokar hana fita bayan rikici a Adamawa. Hoto: Governor Ahmadu Umaru Fintiri.
Source: Twitter

Umarnin da Fintiri ya ba jami'an tsaro a Adamawa

A martaninsa game da sabbin hare-hare da suka cigaba a yankin, Gwamna Fintiri ya umurci a sanya dokar hana fita na awanni 24.

Babban sakataren yada labarai na gwamnan, Humwashi Wonosikou, ne ya fitar da sanarwar hakan ga manema labarai da safiyar Asabar.

Ya ce:

“Gwamnati na kallon wadannan tarzomar a matsayin abin da ba za a yarda da shi ba, saboda za ta yi duk mai yiwuwa domin kawo karshen rikicin da ke faruwa.
“An umarci jami’an tsaro su aiwatar da dokar hana fita da tsauri. Duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci."

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda da ke hijira a tsakanin Kebbi da Zamfara

Shawarar da Fintiri ya ba al'ummar Adamawa

Dokar hana fita za ta cigaba da aiki har sai wani sabon umarni ya fito daga gwamnatin jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Gwamna Fintiri ya bukaci mazauna ƙaramar hukumar Lamurde da su kwantar da hankalinsu kuma su guji yada jita-jita a tsakanin juna.

“Gwamnati na da kudirin kare rayuka da dukiya da kuma tabbatar da zaman lafiya ga duka ‘yan kasa."

- Cewar Fintiri

Rikici ya jawo asarar duniyoyi a Adamawa

Mun ba ku labarin cewa sabon rikici ya ɓarke a kauyukan Lafiya da Boshikiri na jihar Adamawa, inda aka ƙone gidajen wasu makera tare da asarar dukiya mai yawa.

Rundunar ‘yan sandan Adamawa ta tabbatar da cewa gidajen da aka ƙone sun haɗa da na Ododumga Kenneth da Nura Haruna inda ta yi Allah wadai da abin da ya faru.

Kwamishinan ‘yan sanda ya yi gargaɗi ga masu tayar da tarzoma da neman haɗin kai daga jama’a don hana cigaban rikici da kama wadanda ake zargin suna da laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.