Peter Obi: Siyasa za Ta Rikita Izala, Jingir Ya Yi wa Yusuf Sambo Zazzafan Raddi
- Shugaban malaman Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi kakkausar suka kan Sheikh Yusuf Sambo bayan ya karɓi Peter Obi a Kaduna
- Hakan na zuwa ne yayin da aka cigaba da maganar siyasa da yunkurowar 'yan adawa da suke kalubalantar Bola Tinubu
- Maganganun Sheikh Jingir sun tayar da kura a kafafen sada zumunta, inda wasu ke kwatanta su da irin tarbar da ya taba yi wa Rochas Okorocha
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateau – Shugaban majalisar malaman Izala na kasa, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi huduba mai zafi game da ziyarar da Peter Obi ya kai wa mataimakinsa.
Maitaimakin shugaban Izala na kasa, Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachukun ya karbi Peter Obi a jihar Kaduna.

Source: Facebook
Hamza Muhammad Sani ne ya wallafa bayanin da Sheikh Jingir ya yi a wani bidiyo da ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
'Yan Najeriya sun fara nuna wanda suke so jam'iyyar haɗaka ADC ta tsayar takara a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon ɗan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar LP, Peter Obi ya ziyarci malamin ne domin bayar da gudunmawa ga makarantar da ya gina, inda ya miƙa tallafin kuɗi.
Jingir ya yi Allah wadai da tarbar Obi
A ranar Juma’a, 11 ga Yuli, Sheikh Jingir ya yi huduba wacce ta ƙunshi suka mai tsanani ga Sheikh Yusuf Sambo.
Ya bayyana cewa bai kamata malamin ya karɓi Peter Obi ba, duba da tarihin siyasa da alaka da yankin da Obi ya fito.
Sheikh Jingir ya ce Obi dan kabilar Ibo ne, kabila da ake alakanta da kisan Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello, a lokacin juyin mulki na 1966.
Ya kara da cewa idan Sheikh Yusuf Sambo ba zai iya bin tafiya da biyayya ba, to zai iya fita daga tafiyar, yana mai bayyana hakan a matsayin tawaye.
Goyon bayan gwamnati da sukar Obi
Sheikh Jingir ya kuma jaddada goyon bayansa ga gwamnatin Bola Tinubu da Kashim Shettima, yana yabawa tsarin tikitin Muslim-Muslim da suka ci zabe da shi a 2023.
Peter Obi da ke daya daga cikin manyan abokan hamayyar Tinubu a zaben da ya gabata, ya samu karbuwa a yankunan Kudu da wasu sassan Arewa.
Sheikh Yusuf Sambo bai ce komai ba
Duk da yadda zancen ya yi zafi kuma ya dauki hankalin al'umma da dama, Sheikh Yusuf Sambo bai ce komai ba har yanzu.
Sai dai Salim Yusuf Sambo ya wallafa bidiyon da ke nuna lokacin da Sheikh Jingir ya karɓi Rochas Okorocha, dan kabilar Ibo kuma tsohon gwamnan jihar Imo a Jos, a Facebook.
Wannan ya haifar da ce-ce-ku-ce inda wasu ke ganin cewa maganganun Sheikh Jingir na da fuska biyu, yayin da wasu ke goyon bayansa bisa dalilan tarihi da siyasa.
Zancen ya ci gaba da daukar hankali a shafukan sada zumunta, musamman ta bangaren siyasa da addini, inda al’umma ke ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu.

Source: Facebook
An zauna da Sheikh Triumph a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta zauna da fitaccen malamin addini, Sheikh Abubakar Lawal Triumph.
Hakan na zuwa ne bayan wani wa'azi da Sheikh Abubakar Lawal Triumph ya yi ya tayar da kura a fadin jihar.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano ya bukaci duk wasu korafi kan maganar da malamin ya yi su kai kara wajen da ya dace.
Asali: Legit.ng
