Bayan Nasara a Kotun Koli, Gwamna Ya Jajubo Binciken Gwamnatin da Ya Gada
- Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya fadi matakin da zai ɗauka kan gwamnatin da ta shude bayan samun nasara a kotun koli
- Okpebholo ya ce zai binciki yadda tsohon gwamna, Godwin Obaseki ya kashe kudin gwamnati ba bisa ka'ida ba
- Ya ce Obaseki ya biya Naira biliyan 8 kan tsarin kwamfuta, amma gwamnatin yanzu ta kori masu kwangilar, ta horar da ma'aikatan cikin gida
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Benin-City, Edo - Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo ya shirya binciken tsohuwar gwamnatin da ta shude.
Okpebholo ya bayyana shirin bincikar yadda tsohon gwamna Godwin Obaseki ya tafiyar da kudaden jihar ba bisa ka'ida ba.

Source: Facebook
Gwamna Okpebholo zai binciki gwamnatin Obaseki
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake jawabi ga shugabannin jam’iyya, matasa, ma’aikata da ‘yan kasuwa a Benin, cewar Punch.
Wannan jawabi ya biyo bayan dawowar Okpebholo daga Abuja, bayan Kotun Koli ta tabbatar da nasararsa a zaben gwamna na 2024.
Okpebholo ya zargi gwamnatin Obaseki da amfani da ‘yan kwangila da yawa, yana cewa hakan ya sa aka wawure kudin asusun jihar.
Ya ce gwamnatinsa ta gano cewa an biya wani dan kwangila N6bn da karin N2bn akan “manhaja” da za a iya kirkira cikin gida.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kirkiro manhajarta, ta kuma kori dan kwangilar domin rage kashe kudin gwamnati.
Okpebholo ya ce:
“Na umurci a horas da ma’aikatanmu domin su dinga aikin. Mun kori dan kwangilar, muna rage yawan kashe kudi yanzu.
“Ma’aikatanmu sun cancanta sosai, amma Obaseki ya fi amfani da ‘yan kwangila maimakon ma’aikatanmu da ke da ilimi.”
Ya ce za a duba yadda aka kashe kudade da kuma irin mulkin Obaseki a tsawon shekaru takwas da ya yi a kan mulki, Vanguard ta ruwaito.
“Sun gama fada da mu, yanzu lokaci ne na mayar da martani kuma za mu hukunta wadanda suka ci amanar jama’a.”
- Cewar Okpebholo

Source: Twitter
An yabawa Okoebholo kan jagorantar jam'iyyar APC
Mataimakin gwamna, Dennis Idahosa, ya yaba wa Okpebholo da jajircewarsa wajen jagorantar jam’iyya a lokacin shari’a.
Sai dai, wasu daga cikin magoya bayan Okpebholo sun ce an hana su shiga fadar gwamnati duk da sun tarbe shi a filin jirgi.
Magoya bayan sun hadu tun da sassafe a filin jirgin sama na Benin don maraba da Okpebholo bayan nasararsa a kotu.
Gwamnan ya isa filin jirgin sama misalin 12:40 na rana, inda aka tarbe shi da farin ciki da wakoki na goyon baya.
Tinubu ya taya Okpebholo murnar nasara a kotu
Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya gwamnan Edo, Monday Okpebholo da APC murna bayan sun yi nasara a kotu.
Bayan zaben gwamnan jihar da aka gudanar a shekarar 2024 ne aka shiga shari'a da PDP da dan takararta, Asue Ighodalo.
Shugaban kasar ya bukaci gwamnan da ya hada kan al’ummar Edo tare da ci gaba da gudanar da mulki nagari da aka zaɓe shi ya yi.
Asali: Legit.ng

