Kotu ta Nemi a Cafke Hamdiyya Sidi da Ta 'Ci Mutuncin' Gwamnan Sokoto
- Kotun Wurno da ke Gwiwa a Sokoto ta bayar da sammacin kama Hamdiyya Sidi Sharif duk da rashin lafiyar da ta hana ta halarta kotu
- Kungiyar Amnesty International ta bayyana damuwa kan wannan sammaci da ta ce ya saba wa adalci da ka’idar sauraron ƙara
- Hamdiyya na fuskantar shari’a bisa zargin cin mutunci da tayar da hankali sakamakon suka da ta yi wa gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto– Kotun majistare da ke Wurno, karamar hukumar Gwiwa a jihar Sokoto, ta bayar da sammacin kama Hamdiyya Sidi Sharif.
Hamdiyya Sidi dai wata matashiya ce da ke fuskantar shari’a bisa zargin amfani da kalaman batanci da tayar da hankali.

Source: Facebook
Kungiyar Amnesty International mai kare hakkin dan Adam ce ta sanar da haka a wani sako da ta wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sammacin kama ta ya zo ne a ranar 10 ga Yuli 2025, bayan da Hamdiyya ta gaza halartar zaman kotu na baya saboda rashin lafiyar da take fama da ita tun bayan sace ta.
Kungiyar kare hakkin bil’adaman ta bayyana matakin kotun a matsayin wanda ya saba da ka’idar adalci, inda ta bukaci a soke sammacin har sai an saurari bukatar lauyoyinta.
Abin da ya janyo shari’ar Hamdiyya
Hamdiyya Sidi Sharif na fuskantar shari’a ne bayan ta soki yadda gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ke tafiyar da sha’anin tsaro a yankin Gabashin jihar.
Gwamnatin jihar Sokoto ta gurfanar da ita bisa zargin amfani da kalmomin cin mutunci da kuma tayar da tarzoma, zargin da Amnesty ke kallon yunkuri ne na hana fadin albarkacin baki.
Hamdiyya dai ta bayyana cewa ta na amfani da damar fadin ra’ayi ne domin jawo hankalin gwamnati kan kashe-kashen da hare-haren da ke addabar al’ummar Gabashin jihar Sokoto.
An sace Hamdiyya sau 2 a Sokoto
Tun bayan fara shari’arta, an sace Hamdiyya sau biyu. A karon farko, an bayyana ta a matsayin wadda aka rasa a ranar 20 ga Mayu 2025, yayin da ta tafi kasuwa domin sayen kayan abinci.
A rana ta biyu, an same ta a dajin jihar Zamfara cikin mawuyacin hali bayan masu garkuwa da mutane sun jefar da ita.
A ranar 13 ga Nuwamba 2024, wasu gungun ’yan bindiga sun sake sace ta yayin da take kokarin ɗauko wayarta a wajen caji. Sun yi mata dukan tsiya sannan suka jefar da ita.

Source: Facebook
Kungiyar Amnesty International ta ce maimakon a dinga amfani da karfin iko don dakile masu sukar gwamnati, kamata ya yi gwamnati ta fi maida hankali wajen dakile matsalolin tsaro.
An nemi Tinubu ya shiga shari'ar Hamdiyya
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Amnesty International da wasu kungiyoyin fararen hula sun yi magana kan shari'ar Hamdiyya Sidi.
An bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya shiga harkar domin kawo karshen shari'ar da samar da kwanciyar hankali ga matashiyar.
Sun yi magana ne bayan wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun sace matashiyar da aka same ta a jihar Zamfara.
Asali: Legit.ng


