Abin Ɓoye Ya Fito Fili: An Faɗi Dalilin Rufa Rufa kan Rashin Lafiyar Buhari a Mulkinsa
- Tsohon hadimin shugaban kasa, Garba Shehu ya fayyace labarin berayen fadar shugaban kasa a mulkin Muhammadu Buhari
- Garba Shehu ya ce hakan ya zama dabara don karkatar da hankali daga lafiyar Buhari lokacin dawowarsa daga jinya a London
- A cewar Garba Shehu, ya fadi labarin ne bayan wata shawara da aka yi kan wata waya da aka ce beraye sun cinye
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya yi magana kan rashin mai gidansa.
Garba Shehu ya bayyana cewa labarin berayen da suka mamaye fadar shugaban kasa karya ce don kaucewa maganar rashin lafiyar Buhari.

Source: UGC
Garba Shehu ya tona gaskiya kan jinyar Buhari
Garba Shehu ya fadi haka a cikin littafinsa da aka ƙaddamar da shi a Talata a Abuja, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu ya bayyana cewa ya kirkiri labarin mamayar beraye a fadar shugaban kasa ne don karkatar da hankalin jama’a daga tambayoyi kan lafiyar shugaban kasa Buhari.
Kafin dawowar Buhari Najeriya a 2017, bayan fiye da wata uku yana jinya, shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, ya zargi cewa an maye gurbinsa da wani mai suna Jibrin daga Sudan.
Yadda aka taso gwamnati lokacin jinyar Buhari
Bayan dawowarsa, wasu ‘yan Najeriya sun fara tambaya ko lallai shi ne ko kuma wannan clone din ne kamar yadda Kanu ya yi ikirari.
Lamarin ya kara daukar hankali ne bayan fadar shugaban kasa ta sanar cewa Buhari zai dinga aiki daga gida maimakon ofishinsa, abin da ya ƙara haifar da shakku game da lafiyarsa.
Shehu ya ce:
“A cikin sa’o’i kaɗan da shugaban ya dawo, na ji wata tattaunawa a ofishin shugaban ma'aikata, inda aka ce an samu matsala da wata waya.
“Wani ya yi zato cewa beraye ne suka yi sanadiyyar hakan, ganin cewa ofishin ya daɗe ba a amfani da shi.
“Da tambayoyi suka yi yawa game da dalilin da ya sa shugaban kasa zai dinga aiki daga gida idan har yana da lafiya, sai na gaya wa ‘yan jarida cewa ofishin yana bukatar gyara saboda beraye sun ci waya.”

Source: Depositphotos
Dalilin Garba Shehu na shirya labarin
Garba Shehu ya tuna cewa labarin beraye da suka lalata kayayyaki da na’urar sanyaya daki a fadar shugaban kasa ya bazu a duniya, cewar The Guardian.
Tsohon kakakin fadar shugaban kasa ya kara da cewa:
“Da ‘yan jarida suka nemi ƙarin bayani, kiran waya ya karu, har BBC Hausa ta tambaye ni irin berayen da ke cin waya.
“Don su daina matsa min, sai na ambato berayen da suka shiga kasar nan a shekarun 1980 lokacin jiragen ruwa masu dauke da shinkafa daga Kudu maso Gabas.”
“Shekaru bayan haka, wasu sun yi dariya da wannan labari, kuma kadan ne kawai suka gaskata."
Jonathan ya zargi gwamnatin Buhari da gallazawa
Kun ji cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce gwamnatin Buhari ta gallaza wa mukarraban gwamnatinsa kan shari’ar OPL-245.
Shugaba Jonathan ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da littafin tsohon ministan shari'a na lokacinsa, Bello Adoke.
Goodluck Jonathan ya ce adalci da gaskiya ne tubalan ci gaban kowace kasa, don haka ya bukaci shugabanni su rike wadannan dabi'u.
Asali: Legit.ng

