Darajar Annabi SAW: 'Yan Sandan Kano Sun Gayyaci Sheikh Lawan Triumph
- Rundunar ‘yan sandan Kano ta bukaci jama’a su kwantar da hankali dangane da ce-ce-ku-cen da wa’azin Sheikh Abubakar Lawan Triumph ya haifar
- Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya gayyaci Sheikh Lawan Triumph tare da fara tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki don hana rikici
- Bayan zaman da aka yi, an ja hankalin jama’a da su guji tada zaune tsaye da maganganun da ka iya tayar da hankali a kafafen sada zumunta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankali tare da guje wa duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali.
Ta yi magana ne dangane da muhawarar da ta taso kan wa’azin Sheikh Abubakar Lawan Triumph.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da rundunar 'yan sandan ta yi ne a cikin wani sako da SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganawar ta biyo bayan wani jawabi game da Annabi SAW da Sheikh Triumph ya yi wanda ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu kungiyoyi da mabambantan ra’ayoyi a kafafen sadarwa.
Sanarwar ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ne ya gayyaci Sheikh ɗin don tattaunawa da sauran masu ruwa da tsaki.
Dalilin 'yan sanda na gayyatar Sheikh Triumph
A cewar sanarwar, kwamishinan ‘yan sanda ya fara tuntubar wakilan gwamnati, shugabannin addinai da na al’umma domin samun fahimta da tabbatar da zaman lafiya.
Sanarwar ta ce wannan mataki na da nufin dakile yiwuwar rikici tare da tabbatar da cewa kowa na amfani da ‘yancinsa cikin gaskiya da bin doka.
'Yan sanda sun ce yana da muhimmanci kowa ya mutunta ra’ayoyin juna, ya guji tada hankali, da amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ta dace.

Source: Facebook
An gargadi jama’a kan amfani da intanet
Rundunar ta shawarci jama’a da su daina wallafa kalaman da za su iya tayar da hankali ko janyo fitina.
'Yan sanda sun bukaci duk wanda ke da korafi ya kai shi ga hukuma maimakon ɗaukar doka a hannu.
Sanarwar ta ce:
“Mun jajirce wajen ganin an samu zaman lafiya da adalci a jihar Kano ba tare da nuna bambanci ba,”
Kiyawa ya ce rundunar na bukatar hadin kan jama’a domin tabbatar da daidaito da kwanciyar hankali a cikin al’umma.
Bukatar hadin kai da zaman lafiya a Kano
Rundunar ‘yan sandan ta ce tana da cikakken kwarin gwiwa wajen kare rayuka da dukiyoyi, kuma za ta ci gaba da sanya idanu don ganin cewa ba a bar kowa ya lalata zaman lafiya ba.
An kuma bukaci al’umma su ci gaba da aiki tare da jami’an tsaro don gina kyakkyawar mu’amala da juna, tare da girmama juna ba tare da keta doka ba.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda da ke hijira a tsakanin Kebbi da Zamfara
Za a yi sallar rokon ruwa a jihar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa kwamitin majalisar malamai na jihar Kano ya bukaci al'ummar Musulmi su fito sallar rokon ruwa.
Rahotanni sun nuna cewa shugaban majalisar, Sheikh Ibrahim Khalil ne ya fitar da sanarwa a fadin jihar.
Ana sa ran dukkan al'ummar Musulmi za su amsa kiran domin rokon Allah ya azurta jihar Kano da ruwan sama.
Asali: Legit.ng

