Jonathan Ya Zargi Buhari da Gallazawa Jami'ansa kan Badakalar Malabu

Jonathan Ya Zargi Buhari da Gallazawa Jami'ansa kan Badakalar Malabu

  • Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce gwamnatin Buhari ta gallaza wa mukarraban gwamnatinsa kan shari’ar OPL-245
  • Shugaba Jonathan ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da littafin tsohon ministan shari'a na lokacinsa, Bello Adoke
  • Goodluck Jonathan ya ce adalci da gaskiya ne tubalan ci gaban kowace kasa, don haka ya bukaci shugabanni su rike wadannan dabi'u

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari, da gallaza wa wasu manyan jami’an gwamnatinsa kan badakalar Malabu.

Jonathan ya bayyana hakan ne ta bakin tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, a wajen kaddamar da littafin tsohon babban lauyan gwamnati, Bello Adoke, a Abuja.

Goodluck Jonathan tare da shugaba Buhari a shekarun baya.
Goodluck Jonathan tare da shugaba Buhari a shekarun baya. Hoto: Garba Shehu
Source: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa littafin da aka kaddamar din ya bayyana abubuwan da suka faru a badakalar da ta janyo ce-ce-ku-ce da shari’u a kasashen duniya.

Kara karanta wannan

An hango Kashim Shettima, Kwankwaso, El-Rufa'i da Saraki tare a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan ya kare Adoke daga zarge-zarge

Jonathan ya ce Adoke da ya yi aiki a matsayin Ministan Shari’a a mulkinsa, ya fuskanci gallazawa da tsangwama daga gwamnatin Buhari saboda rawar da ya taka a cinikin OPL-245.

A cewar shi:

“Bayan na sauka a 2015, gwamnatin da ta karbi mulki ta fara wani abin da jama’a da dama suka kwatanta da farautar mukarraban gwamnatina,”

Tribune ta wallafa cewa ya kara da cewa:

“Adoke wanda ya rubuta wannan littafi, shi ne Ministan Shari’a a lokacin. An bi shi kowane lungu da sako a duniya saboda wannan lamari.
"Amma yau yana raye, yana lafiya, kuma yana nan ya ba da labarinsa.”

"Adalci da gaskiya ne tushen cigaba,' Jonathan

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa babu wata al’umma da za ta ci gaba ko ta samu zaman lafiya idan ba ta gina kanta bisa gaskiya da adalci ba.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Majalisa ta kira gwamna, tsofaffin gwamnoni da jami'an tsaro kan kashe kashe

“A ko’ina a duniya, an yarda cewa al’umma ko kungiya da ba ta mutunta gaskiya da adalci ba, ba za ta samu ci gaba ko zaman lafiya ba.”

Jonathan ya kuma bukaci masu rike da madafun iko a kasar nan da su rungumi gaskiya da kuma adalci a ayyukansu na yau da kullum.

Tarihin badakalar Malabu OPL-245

Badakalar OPL-245 ta samo asali ne tun shekarar 1998 lokacin da gwamnatin marigayi Sani Abacha ta bai wa kamfanin Malabu Oil da Gas lasisin hako mai a wani gagarumin filin mai.

A shekarar 2011 ne Malabu ta sayar da mallakinta ga kamfanonin Shell da Eni da suka biya dala biliyan 1.3.

Manyan baki yayin kaddamar da littafin Adoke kan badakar Malabu
Manyan baki yayin kaddamar da littafin Adoke kan badakar Malabu. Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

Sai dai daga baya aka bankado cewa akalla dala biliyan 1.1 daga cikin kudin sun shiga hannun jami’ai da ‘yan siyasa ta hanyar cin hanci.

Wannan lamari ya janyo shari’u da bincike a Najeriya da kasashen waje, inda aka dade ana jan kafa tsakanin gwamnati da wadanda suka yi mu’amala da kudin.

Saraki ya yaba wa ministan Jonathan, Adoke

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa ya yaba wa tsohon ministan shari'a, Bello Adoke kan wallafa littafi.

Kara karanta wannan

Littafi: Garba Shehu ya tara Gowon, Atiku, Osinbajo, El Rufa'i, Aminu Ado a Abuja

Bello Adoke ya wallafa littafin ne domin warware wasu radani da aka samu a lokacin da ya ke minista a gwamnatin Jonathan.

Taron kaddamar da littafin ya samu halartar manyan 'yan siyasa da suka hada da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng