Sojoji Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'adda da ke Hijira a tsakanin Kebbi da Zamfara

Sojoji Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'adda da ke Hijira a tsakanin Kebbi da Zamfara

  • Sojojin sama sun kai hari ga ‘yan bindiga a kan hanyar Kebbi–Zamfara, inda suka hallaka da dama daga cikin su
  • An hango gungun ‘yan ta’adda dauke da babura 150 ta, wanda ya taimaka wa jiragen yakin NAF su kai masu luguden wuta
  • Dakarun kasa sun kammala farmaki da safiyar 10 ga Yuli, inda suka tarar da gawarwakin ‘yan ta’adda da makamai da dama

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi – Dakarun sojin saman Najeriya da ke karkashin Operation Fansan Yamma sun yi luguden wuta a kan wasu gungun ‘yan bindiga.

Rahotannin sun bayyana cewa an hango yan ta'addan da ke yawo da babura a kan hanyar Kebbi zuwa Zamfara, inda suka hallaka da dama daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Harin ƴan bindiga: Mutane sun ji azaba, sun fara tserewa daga gidajensu a Filato

Sojojin Najeriya a bakin aiki
Sojojin Najeriya sun kai hari kan yan ta'adda Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa hare-haren sun auku ne kusa da kauyen Yarbuga da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Sojoji sun fatattaki yan bindiga

Daily Trust ta ruwaito cewa kakakin rundunar sojin sama, Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa rundunar ta samu sahihan bayanan sirri a kan 'yan ta'addan.

Rahotannin sun ce akwai wasu gungun ‘yan bindiga da ke tafe da kusan babura 150, kowanne dauke da mutum biyu masu makamai.

Ya ce an yi amfani da fasahar na'urorin leƙen asiri kai tsaye wajen gano su, kafin jiragen yakin NAF su kai musu hari.

Ejodame ya bayyana cewa:

“A ranar 9 ga Yuli, 2025, an gudanar da hare-haren sama da suka yi wa gungun ‘yan bindiga mummunar illa a hanyar Kebbi–Zamfara.”
“Bincike na bayanan leƙen asiri ya nuna motsin gungun da ke tafe da babura 150, kowanne dauke da akalla ‘yan ta’adda biyu, kusa da Yarbuga a karamar hukumar Maru.”

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan acaba za su yi fito na fito da 'yan sanda, hukuma ta yi gargadi

Sojoji sun yi wa 'yan ta’adda barna

Ejodame ya ce hotunan bidiyon da aka dauka daga sama sun nuna wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun tsere da kafa, wasu kuma a babura.

Taswirar jihar Kebbi
An kashe yan ta'adda da dama a Kebbi Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce amma jiragen yakin NAF sun sake binsu tare da ci gaba da kai musu hari a yayin da suke kokarin tserewa.

Ya ce:

“Bayan harin sama, dakarun kasa sun kai samame zuwa kauyen Yarbuga da safiyar ranar 10 ga Yuli, 2025.”
“A wurin, an tarar da gawarwakin ‘yan ta’adda da dama da makamai da suka bari a baya, tare da babura masu yawa da suka kone kurmus.”

Ejodame ya jaddada cewa wannan hadin gwiwar sojojin sama da na kasa ya yi mummunar illa ga karfin ‘yan ta’adda a yankin.

'Yan bindiga sun yi gumurzu da sojoji

A baya, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya, da ke Zuru a jihar Kebbi, ta yi nasarar dakile wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai a garin Ribah.

Kara karanta wannan

An gwanza fada a Filato, an kashe 'yan banga 70 da kona gidaje

Harin ya faru ne ranar Laraba, inda ‘yan bindiga fiye da 400 dauke da mugayen makamai suka kutsa cikin garin Ribah da nufin kwace shi gaba daya.

Rahoton ya ce an kashe da dama daga cikin ‘yan ta’addan, duk da cewa wasu daga cikinsu sun kwashe gawarwakin abokan su da suka mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng