GDP: ADC Ta Ragargaji Gwamnatin Tinubu kan Murna da Bunkasar Tattalin Arziki
- Jam'iyyar ADC ta caccaki gwamnatin tarayya saboda murna bisa karuwar alkaluman ci gaban tattalin arzikin cikin gida na GDP
- Sanarwar da kakakin jam’iyyar na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar ta bayyana cewa alkaluman ba su nuna halin da talaka ke ciki ba
- Ya ce jama'a sun san akwai matsalolin tattalin arziki, yunwa, rashin ci gaban kasa da matsalar tsaro a Najeriya duk da ikirarin ci gaban da ta yi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Jam’iyyar ADC ta caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa murnar da ta yi kan alkaluman da hukumar 'kididdiga ta fitar kan bunkasar tattalin arziki na GDP.
Jam'iyyar hadakar 'yan adawa ta bayyana cewa alkaluman ba su nuna gaskiyar halin da talakawan Najeriya ke ciki ba a yanzu.

Source: Facebook
Wannan na 'kunshe a cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, aka kuma wallafa a shafin X na ADC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ADC ta caccaki gwamnatin Bola Tinubu
Daily post ta wallafa cewa ADC ta ce yadda gwamnati ta mayar da hankali kan rahoton NBS ya nuna cewa ba ta da niyyar duba ainihin matsalolin yan Najeriya.
Sanarwar ta ce:
“Ba za ka iya lissafin yunwa ba saboda ‘yan Najeriya ba za su ci GDP ba."
Jam’iyyar ta ce yayin da gwamnatin ke ta shelar sababbin bayanai na GDP, miliyoyin ‘yan Najeriya na fama da hauhawar farashin abinci.
ADC ta kara da cewa haka kuma ana fama da karuwar talauci da da rashin ababen more rayuwa tsakanin 'yan Najeriya.
ADC ta ce gwamnatin Tinubu ta gaza
A cewar ADC, 'kididdigar GDP na Najeriya wanda ya kai Dala biliyan 509 a shekarar 2014, yanzu ya dawo Dala biliyan 244.

Source: Twitter
Ta ce wannan ya sa Najeriya ta fado zuwa na hudu, wanda ke nufin ta zo a bayan Afrika ta Kudu, Masar da Aljeriya.
ADC ta ce:
“Wannan ba kawai sabon lissafi ba ne. Shaida ce ta gazawar da gwamnatin APC ta yi wajen tafiyar da tattalin arzikin kasa tsawon shekara 10."
ADC ta bayyana cewa yawan GDP da ya kai Naira tiriliyan 373 ya samo asali ne daga karyewar darajar Naira, ba daga ci gaban da ake bukata ba.
Jam’iyyar ta caccaki gwamnatin Tinubu bisa gazawa wajen cika alkawarin fadada fannonin tattalin arziki kamar noma, masana’antu da fasaha.
Ta ce:
“Babu karuwa a masana’antu, babu karin kudin shiga, babu sauyi a wutar lantarki, lafiya ko tsaro. Abin da muke gani kawai lissafi ne da ba shi da ma’ana."
Jigo a PDP ya koma jam'iyyar ADC
A baya, kun ji cewa C.I.D. Maduabum, tsohon babban daraktan kungiyar gwamnonin PDP kuma tsohon dan majalisar wakilai, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar bisa wasu dalilai.
Maduabum ya bayyana sauya shekar tasa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce rikice-rikicen cikin gida sun hana tsohuwar jam'iyyarsa ci gaban da ya kamata.
Ficewar Maduabum na daga cikin jerin sauya sheka da PDP ke fuskanta tun bayan ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da ya bar jam'iyyar kan zargin rashin adalci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


