Jonathan: Abin da Ya Faru da 'Shugaban Ƙasa' Ya Yi Yunƙurin Tsige Gwamnan Jihar Borno

Jonathan: Abin da Ya Faru da 'Shugaban Ƙasa' Ya Yi Yunƙurin Tsige Gwamnan Jihar Borno

  • Kashim Shettima ya tuna yadda ya zama gwamnan da ya fi baƙin jini a Najeriya lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan
  • Mataimakin shugaban ƙasar ya ce a lokacin, Jonathan ya yi yunkurin tsige shi daga matsayin gwamnan Borno amma wasu muƙarrabansa suka hana
  • Ya yabawa tsohon Antoni Janar na Tarayya, Mohammed Adoke bisa yadda ya nuna juriya wajen goyon bayan gaskiya a lokacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya tuna yadda ya sha wahala har aka yi yunƙurin tsige shi daga mulki lokacin da yake gwamnan Borno.

Shettima ya ce tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan ya yi yunƙurin tunɓuke shi daga kujerar gwamna amma wasu muƙarrabansa suka hana.

Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima.
Yadda Shettima ya kusa rasa kujerarsa ta gwamnan Borno a tsakanin 2011 zuwa 2015 Hoto: @OfficialSKSM
Source: UGC

Kashim Shettima, wanda tsohon gwamnan jihar Borno ne, ya bayyana haka ne a Abuja ranar Alhamis, a wurin kaddamar da wani littafi, kamar yadda Punch ta kawo.

Kara karanta wannan

'APC, PDP, ADC, duk ɗaya ne': Shettima ya tura saƙo ga ƴan adawa ana batun haɗaka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan kusoshi sun halarci ƙaddamar da littafin mai suna "OPL 245: Inside Story of the $1.3bn Nigeria Oil Block", wanda tsohon Antoni Janar na Tarayya, Mohammed Adoke, ya wallafa.

Yadda Jonathan ya so tsige gwamnan Borno

Shettima, ya bayyana cewa shi ne mutumin da aka fi ƙyama a bainar jama’a a ƙarshe-ƙarshen mulkin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.

“A cikin shekaru huɗu na ƙarshe na gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, ni ne mutum mafi baƙin jini a idon jama’a, ni ne maƙiyim jama’a na ɗaya.”
“Akwai wasu mutanen kirki biyu da suke zaune a nan. Ba ko da yaushe ake ba da shawarwari na kirki a tsakanin shugaban ƙasa, mataimakinsa, shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilai ba.”
“Tsohon shugaban ƙasa Jonathan, wanda yanzu mun gyara dangantakarmu, ya bayyana ra’ayinsa na tsige gwamnan Borno a wancan lokacin.”

- Kashim Shettima.

Me ya hana tsige Shettima daga gwamnan Borno?

Kara karanta wannan

An hango Kashim Shettima, Kwankwaso, El-Rufa'i da Saraki tare a Abuja

Shettima ya ƙara da cewa kakakin Majalisar Wakilai na lokacin, Rt. Hon. Aminu Tambuwal da Antoni Janar, Muhammed Adoke ne suka gaya wa Jonathan gaskiya.

Mataimakin shugaban ƙasa ya ci gaba da cewa:

"Aminu Tambuwal, wanda shi ne shugaban majalisar wakilai a lokacin, ya ce masa 'Mai girma shugaban ƙasa, ba ka da ikon tsige ko kansila da aka zaɓa.”
"Duk da haka, Jonathan bai yarda ba har ya sake tada batun a zaman Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, inda Adoke ya shaida masa cewa hakan ya saɓa wa tsarin mulki.
"Adoke ya gaya wa shugaban ƙasa cewa ba ka da ikon tsige gwamna balle ma kansila. Daga nan suka nemi ra’ayin lauya kuma mamba a majalisar, Kabiru Turaki (SAN), wanda ya goyi bayan Adoke. Haka aka kashe batun."
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.
Shettima ya yabawa Adoke ta hana tsige shi a lokacin yana gwamnan Borno Hoto: @officialSKSM
Source: Twitter

Kashim Shettima ya yabawa Adoke saboda juriya da ƙarfin hali da ya nuna wajen tsayawa akan gaskiya, kamar yadda Channels tv ta kawo.

Shettima ya buƙaci haɗin kan ƴan siyasa

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya nuna cewa duka ƴan siyasa ɗaya suke idan ana batun aikin gina ƙasa.

Kara karanta wannan

Tsohon na kusa da Atiku ya yi masa wankin babbn bargo kan taksrar shugaban kasa

Sanata Shettima ya shaidawa ‘yan siyasa a Najeriya cewa dukkansu daya suke wajen gina kasa, duk da banbancin jam'iyyun siyasa.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a taron kaddamar da littafin Mohammed Adoke, wanda manyan jiga-jigan siyasar ƙasar nan suka halarta a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262