Gwamna Abba Ya Nada Sabon Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Kano

Gwamna Abba Ya Nada Sabon Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Kano

  • Gwamnan jihar Kano, mai girma Abba Kabir Yusuf ya yi sabon naɗin muƙami a gwamnatinsa
  • Abba Kabir Yusuf ya naɗa sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar watanni shida bayan soke ofishin
  • A cewar mai magana da yawun gwamnan an dawo da ofishin ne domin ci gaba da inganta ayyukan gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya naɗa sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗa Dr. Suleiman Wali Sani, mni, a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano.

Gwamna Abba ya yi sabon nadi a gwamnatinsa
Gwamna Abba ya nada shugaban ma'aikatan fadar gwamnati Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ofishin shugaban ma’aikatan dai an soke shi a watan Disamba bayan cire Shehu Wada Sagagi daga kujerar, wanda daga baya aka naɗa shi a matsayin kwamishinan ma’aikatar kasuwanci da zuba jari.

Kara karanta wannan

Kudirin ƙirƙiro karin jiha 1 a Arewacin Najeriya ya samu gagarumin goyon baya a Majalisa

Gwamna Abba ya naɗa shugaban ma'aikata

A cewar mai magana da yawun gwamnan, dawo da ofishin shugaban ma’aikatan wani ɓangare ne na ƙoƙarin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi domin ƙarfafa shugabanci da inganta isar da ayyuka ga al’ummar Kano.

Dr. Suleiman Sani, ƙwararren likita ne, masanin tsare-tsare, kuma tsohon babban sakatare, ya shafe fiye da shekaru 40 yana hidimar gwamnati cike da ƙwarewa da ƙwazo.

Kafin wannan sabon naɗin, yana aiki a matsayin mai bai wa gwamna shawara kan harkokin ma’aikata.

Dr. Suleiman Wali Sani ya kammala karatunsa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya samu digirin MBBS a fannin likitanci.

Ya ƙara samun ƙwarewa a fannin shugabanci da difloma daga jami’ar Bayero ta Kano da kuma shaidar mni daga kwalejin nazarin tsare-tsare da dabarun gudanarwa ta ƙasa (NIPSS), Kuru.

A tsawon shekaru, ya riƙe muhimman muƙaman gudanarwa da dama, ciki har da darakta janar a ma’aikatu kamar na lafiya da kasuwanci, sakataren zartarwa da babban sakatare a hukumomin gwamnati masu mahimmanci.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya fadi damar da Atiku ya rasa ta zama shugaban kasa

Haka kuma, ya shugabanci manyan asibitoci na jihar irin su asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da asibitin ƙwararru na Muhammad Abdullahi Wase a matsayin babban daraktan likitoci.

Gwamna Abba ya yi nade-nade a gwamnatinsa
Gwamna Abba ya nada shugaban ma'aikatan fadar gwamnati Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamna Abba ya yi naɗi a gwamnati

Hakazalika Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma naɗa wani gwarzon jami’in soja mai ritaya, Manjo Janar Mohammed Sani a matsayin darakta janar na ayyuka na musamman na gidan gwamnatin Kano.

Manjo Janar Mohammed Sani, gogaggen jami’in soja ne wanda ya riƙe muƙamai da dama na manyan shugabanci da gudanarwa a lokacin aikinsa.

Ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, warware rikice-rikice da kuma aiwatar da ayyukan tsaron ƙasa kafin ya yi ritaya.

Gwamna Abba ya ba Sarkin Lafia muƙami

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa sabon shugaban jam'iar North-West.

Gwamna Abba ya naɗa Sarkin Lafiya, mai martaba Sidi Muhammad Bage a muƙamin shugabancin jami'ar.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya naɗa basaraken ne domin ƙarfafa dangantaka tsakanin sarakuna da cibiyoyin ilmi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng