"Da Aiki a Gabanka," Tinubu Ya Tura Saƙo ga Gwamna Edo bayan Nasara a Kotun Koli

"Da Aiki a Gabanka," Tinubu Ya Tura Saƙo ga Gwamna Edo bayan Nasara a Kotun Koli

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya gwamnan Edo, Monday Okpebholo da APC murna bayan sun yi nasara a kotu
  • Bayan zaben gwamnan jihar da aka gudanar a shekarar 2024 ne aka shiga shari'a da PDP da dan takararta, Asue Ighodalo
  • Shugaban kasar ya bukaci gwamnan da ya hada kan al’ummar Edo tare da ci gaba da gudanar da mulki nagari da aka zaɓe shi ya yi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo – Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo murna kan tabbatar da nasararsa a zaben gwamna da Kotun Koli.

A watan Satumba na shekarar 2024 ne aka gudanar da zaben gwamnan jihar Edo, inda Hukumar zabe ta INEC ta ayyana Okpebholo na APC a matsayin wanda ya yi nasara.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya yi martani kan hukuncin Kotun Koli, ya tura sako ga 'yan adawa

Shugaban kasa, Bola Tinubu da Monday Okpepholu
Tinubu ya taya Okpepholu murnar nasara a kotu Hoto: Bayo Onanuga/Edo government house
Source: Facebook

A sakon da hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X, ya ce wannan nasara da gwamnan ya samu a kotu ta yi daidai kuma ta cancanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya bukaci Okpebholo ya hada kan al’umma

Shugaba Tinubu ya bukaci Gwamna Okpebholo da ya nuna karimci tare da mayar da hankali wajen gudanar da mulki nagari domin ci gaban jihar Edo.

Ya kuma shawarce shi da ya hada kan al’ummar jihar daga kowane bangare don cimma buri guda na inganta ci gaban jihar.

A cewar sanarwar:

“Yanzu da gwamnan ya wuce dukkanin ƙalubalen shari’a, lokaci ya yi da zai kara zage damtse wajen kawo sauyi ta hanyar mulki nagari da ayyuka na ci gaba ga al’ummar jihar Edo, kamar yadda ya riga ya fara.”

Edo: Tinubu ya taya APC murna

Shugaban kasa Tinubu ya kuma taya shugabanni da yan jam’iyyar APC a jihar Edo murna kan wannan nasara.

Kara karanta wannan

Tsohon makusancin Obi ya fadi yadda ADC za ta mikawa Tinubu nasara a 2027

Ya bukace su da su hada kai da jajircewa wajen aiwatar da amanar da al’umma suka dora musu na shugabanci.

Shugaban kasa, Bola Tinubu
Tinubu ya taya APC murna kan hukuncin kotu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Hukuncin da kotu ta yanke a zaben Edo

A ranar 10 ga watan Yuli ne dai alkalan kotun koli mai mutum biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba Lawal ya yanke hukunci kan shari'ar zaben Edo.

Sun bayyana cewa masu kara, wato jam’iyyar PDP da dan takararta Asue Ighodalo sun kasa tabbatar da hujjojin da suka gabatar kan rashin bin doka yayin zabe.

Kotun ta yi watsi da karar bisa rashin cancanta tare da tabbatar da nasarar ɗan takarar APC, Monday Okpepholu a matsayin halastaccen gwamna.

Gwamnan Edo ya yaba da hukuncin kotu

A baya, mun wallafa cewa gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya bayyana matuƙar jin daɗinsa bisa hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a ranar Alhamis, 10 ga Yuli, 2025.

A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Fred Itua, ya fitar, Gwamna Okpebholo ya bayyana hukuncin a matsayin wani muhimmin matakin kawo ci gaba.

Ya kara da cewa hukuncin da ya tabbatar masa da nasara ya kawo ƙarshen duk wata gardama da ta taso daga zaɓen gwamnan Edo da aka gudanar shekarar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng