An Hango Shettima, Kwankwaso, El-Rufa'i da Saraki Tare a Abuja

An Hango Shettima, Kwankwaso, El-Rufa'i da Saraki Tare a Abuja

  • Rahoto ya nuna cewa tsohon Antoni-Janar na tarayya, Mohammed Bello Adoke ya kaddamar da littafinsa a birnin tarayya Abuja
  • Shahararrun ‘yan siyasa da suka halarci taron sun hada da Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima, Rabiu Kwankwaso da Nasir El-Rufai
  • Mohammed A doke ya bayyana cewa ya yafewa duk wanda ke da hannu a shari’ar da ta bata masa suna dangane da OPL245

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Antoni-Janar na tarayya kuma Ministan Shari’a a Najeriya, Mohammed Bello Adoke ya kaddamar da littafin da ya rubuta a Abuja.

A yayin taron, ya bayyana cewa ya yafewa duk wanda ya taka rawa wajen matsalolin da suka biyo bayan shari’ar OPL245 da suka shafe shi.

Saraki da Kwankwaso yayin kaddamar da littafin Adoke
Saraki da Kwankwaso yayin kaddamar da littafin Adoke. Hoto: Abubakar Bukola Saraki
Source: Facebook

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya wallafa a X cewa ya yi jawabi wajen taron.

Kara karanta wannan

APC: 'Yan siyasar Arewa sun fara neman kujerar Ganduje gadan gadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adoke ya bayyana yafiyar ne yayin kaddamar da littafinsa da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 10 ga Yuli, 2025.

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa ciki har da Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da tsohon Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu duk sun halarci taron.

Adoke ya fadi dalilin rubuta littafin

Adoke ya ce ba cin mutuncin wasu ba ne manufarsa wajen wallafa littafin, illa bayyana gaskiya da kare sunansa da kuma fayyace abubuwan da suka faru a yarjejeniya da ta shafi arzikin kasa.

The Cable ta rahoto ya ce:

“Na rubuta wannan littafi ne domin fayyace tarihi, ba domin in ci zarafin wani ba.
"A yarjejeniyar OPL245 da aka kammala a 2011, na taka rawa a lokacin ne domin kare muradun tattalin arzikin kasa, ko da yake ban kasance cikin wadanda suka fara yarjejeniyar tun a 2006 ba.”

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi magana a karon farko bayan Shugaba Tinubu ya ba shi muƙami a FAAN

Adoke ya zargi hukumar EFCC da boye hujjoji da tsoratar da shaidu domin cimma nasarar gurfanar da shi a gaban kotu.

Ya ce abin takaici ne yadda wasu suka dauki nauyin bata masa suna, har ya rasa mutunci da zaman lafiyar iyalinsa.

Saraki ya yaba da littafin Mohammed Adoke

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana gamsuwarsa da littafin na Adoke.

Saraki ya ce Adoke ya nuna jarumtaka da hangen nesa wajen yin cikakken bayani a kan daya daga cikin manyan rikice-rikicen gwamnati a tarihin Najeriya.

A cewar Saraki:

“Na yaba da yadda Adoke ya rubuta wannan littafi da ya fitar da cikakken bayani bisa shari’a da tsarin gwamnati, musamman a fannin albarkatun kasa.
"Wannan littafi zai zama abin koyi ga masana, ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki na tsawon lokaci.”
Saraki da tsohon shugaban APC wajen kaddamar da littafin Adoke.
Saraki da tsohon shugaban APC wajen kaddamar da littafin Adoke. Hoto: Abubakar Bukola Saraki
Source: Facebook

An kaddamar da littafin Garba Shehu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya kaddamar da littafi a Abuja.

Garba Shehu ya rubuta littafin ne domin bayyana abubuwan da suka faru a fadar shugaban kasa a lokacin Muhammadu Buhari.

Manyan Najeriya da suka hada da Yakubu Gowon, Atiku Abubakar, Yemi Osinbajo, Aminu Ado Bayero sun halarci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng