Najeriya Ta Samu Tallafi Mai Yawa daga Faransa, za a Yi Aiki a Katsina, Sauran jihohi

Najeriya Ta Samu Tallafi Mai Yawa daga Faransa, za a Yi Aiki a Katsina, Sauran jihohi

  • Najeriya ta samu tallafin €100m daga gwamnatin Faransa domin gina cibiyoyin kere-kere a fadin kasar
  • Ministar al’adu da harkokin yawon bude ido, Hannatu Musawa, ta ce za a fara aiwatar da aikin ne a Katsina, Lagos da Abuja
  • Hannatu Musawa ta ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu na da kishin bunkasa tattali ta hanyar fasahar kere-kere

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Abuja - Ministar al’adu, yawon bude ido da fasahar kere-kere, Hannatu Musawa, ta bayyana cewa Najeriya ta samu tallafin Yuro miliyan 100 daga gwamnatin Faransa.

Rahotanni sun nuna cewa Faransa ta ba Najeriya tallafin ne domin bunkasa masana’antun kere-kere a kasar.

Najeriya ta samu tallafi daga Faransa
Najeriya ta samu tallafi daga Faransa. Hoto: @hanneymusawa
Source: Getty Images

Musawa ta bayyana haka ne a wata hira da aka yi da ita a Arise TV a ranar Laraba, inda ta ce kudin za su taimaka wajen kafa cibiyoyi na musamman da za su tallafa wa matasa.

Kara karanta wannan

Wike ya bayar da umarni kan mabarata da masu sana’o’i da suka cika titunan Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musawa ta ce wannan tallafi wani muhimmin mataki ne da zai kara habaka tattalin arzikin kasa, musamman a kokarin da gwamnati ke yi a halin yanzu.

Za a fara da Katsina, Lagos da Abuja

Musawa ta ce za a fara da gina cibiyoyi a Abuja, Lagos da Katsina, kafin daga bisani a fadada aikin zuwa Enugu, Kwara da Akwa Ibom.

A yayin hirar, Hannatu Musawa ta bayyana cewa daga baya za a samar da irin wadannan cibiyoyi a kowace jiha ta Najeriya.

A cewarta:

“Wannan tallafin da muka samu daga gwamnatin Faransa yana nuna irin yadda duniya ke yaba da hazakar matasan Najeriya da abubuwan da muke iya kerawa.
"Wannan dama ce da za ta taimaka mana wajen samar da wuraren horas da matasa da kuma daukar su aiki.”

Halin da tattalin Najeriya ke ciki

Musawa ta bayyana cewa duk da matsin tattalin arzikin da Najeriya ke fama da shi da kuma karancin tallafi, ma'aikatarta ta kasance tana neman hanyoyi da dabaru domin cimma burin ta.

Kara karanta wannan

Katsina: Biki ya koma makoki bayan bindige ɗan shekara 10, an harbi budurwa a kwankwaso

Ta ce:

“Gwamnatin Tinubu na da kishin bunkasa ayyuka da samar da guraben aiki. Don haka, dole ne mu samar da abubuwan more rayuwa da za su ba matasa damar yin fice a fannin kere-kere.”

Sauran ayyukan da za a yi a jihohi

Baya ga cibiyoyin kere-kere, ministar ta kuma bayyana cewa akwai wasu manyan ayyukan da ake aiwatarwa da suka hada da gina wasu wurare na musamman a Abuja da Lagos.

Ta kara da cewa an riga an sanya hannu kan yarjejeniyar gina Creative City, wato birnin fasaha, yayin da aka fara gyaran wasu muhimman dakunan tarihi.

Tinubu da shugaban Faransa, Macron
Tinubu da shugaban kasar Faransa, Macron. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Faransa ta raba tallafin kudi a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Faransa ta amince da raba tallafin kusan Naira biliyan 2 a Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa an raba tallafin kudin ne ga wasu kungiyoyi 19 da suke aikin jin kai a fadin kasar nan.

Yayin raba tallafin a Abuja, gwamnatin Faransa ta tabbatar da cewa an raba kudin ne domin taimako ba tare da wata manufa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng