Littafi: Garba Shehu Ya Tara Gowon, Atiku, Osinbajo, El Rufa'i, Aminu Ado a Abuja
- Tsohon mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya kaddamar da littafin da ya rubuta a Abuja
- Taron ya samu halartar fitattun ‘yan Najeriya da suka hada da Yakubu Gowon, Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai da sauransu
- Littafin na dauke da darussa daga gogewar Garba Shehu a matsayin mai magana da yawun shugaban kasa a lokacin Buhari
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - A ranar Laraba, tsohon mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya kaddamar da littafinsa A Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa an kaddamar da littafin ne mai mai taken According to the President: Lessons From A Presidential Spokesman’s Experience.

Source: Facebook
Garba Shehu ya wallafa a X cewa taron kaddamarwar ya gudana ne a dakin taro na Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja, inda manyan fitattun ‘yan Najeriya suka halarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Littafin yana dauke da bayanai da darussa daga rayuwar Garba Shehu a fadar shugaban kasa, tare da bayani kan siyasar Najeriya a lokacin da ya yi aiki.
Atiku da sauran manya sun halarci taron
Daga cikin wadanda suka halarta akwai tsohon shugaba kasa, Yakubu Gowon; tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Haka zalika, tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya halarci taron, tare da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.
Tsohon shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa karkashin Buhari, Ibrahim Gambari, da mai bai wa Tinubu shawara kan labarai, Bayo Onanuga, su ma sun kasance cikin mahalarta.

Source: Twitter
Sauran manyan kasa da suka halarci taron
Taron ya kuma samu halartar Sarkin Kano na 15; Aminu Ado Bayero kamar yadda ya wallafa a X da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.
Sauran sun hada da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika; ministan yada labarai na yanzu, Mohammed Idris; da tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi.
An kuma ga Nduka Obaigbena, shugaban kamfanin ThisDay da Arise TV, yana daga cikin manyan baki da suka halarci bikin kaddamarwar.
Abubuwan da littafin Garba Shehu ya kunsa
A cewar Garba Shehu, littafin ya kunshi labarai da darussa daga gogewarsa a matsayin mai magana da yawun shugaban kasa, inda ya yi bayani kan yadda ake tafiyar da mulki.
Ya ce littafin zai amfani masu karatu wajen fahimtar salon shugabanci, tsare-tsaren gwamnati da kuma matsalolin da ake fuskanta a lokacin aiki a matsayin wakili na fadar shugaban kasa.
Garba Shehu ya kara da cewa burinsa shi ne ya rubuta tarihi da zai taimaka wajen fahimtar muhimman al’amura da suka faru a lokacin gwamnatin Buhari.
Halin 'yan siyasa a lokacin taro
A Najeriya, bukukuwan kaddamar da littattafai ko wasu ayyukan kai da kai na 'yan siyasa suna kara komawa dandali na siyasa, inda manyan jami'an gwamnati da jiga-jigan jam'iyyun siyasa ke taruwa ba tare da la'akari da bambance-bambancen jam’iyya ba.
Abin da aka saba gani shi ne, irin waɗannan taruka sukan zama wani lokaci na tattara goyon baya da nuna ƙarfin siyasa, musamman yayin da aka gayyato mutane daga jam’iyyun adawa domin su halarci taron.
Misalin haka shi ne taron kaddamar da littafin According to the President da Garba Shehu ya rubuta, inda aka ga fitattun 'yan siyasa daga APC da PDP – irinsu Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, Yemi Osinbajo da sauransu – sun hallara.
Duk da cewa littafin yana da alaƙa da rayuwar aikin Garba Shehu, taron ya zama wata dama ta haɗuwa da tsaffin shugabanni, masu mulki da kuma masu burin komawa mulki.
A wasu lokuta, irin waɗannan taruka sukan zama wata hanya ta sake ƙarfafa dangantaka tsakanin tsofaffin abokan siyasa ko kuma shirya tsaf don sabbin tsarin mulki.
Wannan ya sa ana kallon kaddamar da littafi a Najeriya a matsayin wani ɓangare na dabarun siyasa fiye da na adabi kawai.
Tinubu ya sa Buhari cin zabe a 2015?
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha Gida ya yi bayani kan nasarar da Muhammadu Buhari ya samu a zaben shekarar 2015.
Boss Mustapha Gida ya bayyana cewa babu wani mahaluki a Najeriya da zai bugi kirji ya ce shi ya ba Buhari nasara a lokacin.
Mustapha Gida ya yi magana ne yana martani ga masu gani cewa Bola Ahmed Tinubu ne sanadiyyar nasarar Buhari a zaben.
Asali: Legit.ng


