'Yan Bindiga Sun Gwabza da Jami'an Tsaro, an Rasa Rayukan Mutane da Dama
- Ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
- Miyagun sun kai harin ne a ƙaramar hukumar Mariga inda suka hallaka mutane aƙalla 10 tare da raunata wasu
- Daga cikin mutanen da aka kashe har da jami'an tsaro waɗanda suka yi fito-fito na da ƴan bindigan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Aƙalla mutane 10 ne ciki har da jami'in ɗan sanda da ɗan sa-kai ne suka rasa rayukansu a wani hari da ƴan bindiga suka kai a jihar Neja.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Mangoro da ke ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Source: Facebook
Wasu mazauna yankin sun tabbatarwa da jaridar Daily Trust aukuwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Neja
Sun bayyana cewa tun ranar Talata ne ƴan bindigan suka karɓi iko da Mangoro da wasu ƙauyuka makwabta, bayan sun rinjayi jami’an tsaro da suka haɗa da ƴan sanda da ƴan sa-kai.
Ba a tantance adadin waɗanda suka jikkata ba, ciki har da ƴan sa-kai da suka samu raunukan harbin bindiga.
Wani mazaunin ƙauyen wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya ce ƴan sa-kai da ƴan sanda sun yi ƙoƙari sosai, amma ƴan bindigan sun fi ƙarfinsu.
Ya ce ƴan bindigan waɗanda suka zo da yawa, suna ɗauke ne da muggan makamai.
"Mutane huɗu sun rasa rayukansu, ciki har da ɗan sanda ɗaya, ɗan sa-kai ɗaya da manoma biyu."
"Gaskiya ƴan sanda da ƴan sa-kai sun yi artabu da su, amma sun rinjaye su. A batun gaskiya, harsasan yan sa-kai sun ƙare wanda hakan ya sanya suka gudu."
"Ƴan sa-kai na buƙatar taimako daga hukumomi, musamman na yankin Mangoro, domin wannan hanya ce da ƴan bindigan ke yawan bi.”
- Wata majiya
Wata majiya daban kuma ta bayyana cewa kusa mutane 13 aka kashe, ciki har da ƴan sa-kai, yayin da da dama suka samu rauni sakamakon harbin bindiga.
Majiyar ta kuma ƙara da cewa ƴan bindigan sun lalata turakun sadarwa na wayar salula, lamarin da ya haddasa tsaikon sadarwa a yankin.

Source: Original
Me hukumomi suka ce kan harin?
Shugaban ƙaramar hukumar Mariga, Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya tabbatar da harin, sai dai bai bayyana adadin waɗanda aka kashe ba.
Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Kakakin ƴan sandan ya ce zai bincika ya dawo da bayani, amma bai yi hakan ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Ƴan bindiga sun kai hari a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙaramar hujumar Kafur.
Ƴan bindigan sun hallaka wani malamin addinin Kirista tare da mamban cocinsa a harin da suka kai cikin dare.
Hakazalika sun kuma.yi awon gaba da wata mata zuwa cikin daji a yayin harin wanda suka kai kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Asali: Legit.ng

