An Tafka Babban Asara bayan Mummunar Gobara Ta Cinye Ofishin Jarumai Fina Finai
- Fitacciyar jarumar Nollywood ta bayyana irin jarabawar da ta hadu da ita bayan tashin gobara a ofishinta da ke Lagos
- Iyabo Ojo ta ce ofishinta da ke Legas ya kama da wuta da misalin ƙarfe 7:00 na daren jiya Talata 8 ga watan Yulin 2025
- Iyabo ta wallafa bidiyon gobarar, inda aka ga wani ɓangare na ginin ya ƙone ƙurmus, amma babu rai da ya salwanta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Jarumar Nollywood kuma ‘yar kasuwa, Iyabo Ojo, ta gamu da tsautsayin gobara a ofishinta da ke jihar Lagos.
Iyabo Ojo ta bayyana cewa ofishinta da ke Legas ya kama da wuta a daren ranar Talata 8 ga watan Yulin 2025.

Source: Instagram
Gobara ta kama a ofishin jarumar fina-finai a Lagos
A cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafin Instagram, an ga wani ɓangare na ginin da gobarar ta shafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarta, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na dare a ranar Talata wanda ya jawo asarar dukiyoyi.
Sai dai jarumar fim din ta ce babu wanda ya rasa ransa a cikin wannan mummunan lamari da ya faru.
Iyabo ta gode wa ma’aikatan kashe gobara na jihar Legas da kuma ma’aikatanta bisa gaggawar daukar mataki.
Ta ce:
"Abin nan ya faru ne yau, 8 ga Yuli, 2025 da ƙarfe 7:00 na yamma. Ofishina ya kama da wuta.
"Na gode wa Hukumar Kashe Gobara ta Legas da ma’aikatana da suka ceto abin da ya rage.
"Da yardar Allah, babu wanda ya mutu. Shaiɗan ya so jawo mana, amma Allah ya ce a’a."

Source: Original
Jaruma ta nuna karfin hali bayan gobara
Jarumar da aka fi sani da juriya, ta tabbatar da cewa za ta dawo da ƙarfi fiye da d inda ta yi godiya ga masoyanta kan nuna mata soyayya da goyon baya.
"Da taimakon Allah, zamu dawo da ƙarfi da girma fiye da da."
Cewar Iyabo Ojo
Martanin mutane kan gobarar da ta faru
Mutane da dama sun yi martani kan abin da ya faru inda ake ta yi mata jaje da kuma fatan alheri kan abin da ya same ta.
dona.ld4010:
"Ba a rasa komai ba kuma ba a rasa rai ba, za ki samu fiye da haka kan abin da kika yi asara."
apeke_alasoara:
"Ina karanta martanin mutane kawai sai dariya na ke yi, meye ya haɗa lamarin Mohbad da wannan abin, ba ni da lokacin yi wa mutane martani.
"Mafi yawan masu martani sun tsani matar nan ba tare da dalili ba ba za su taba samun albarka ba."
Gobara ta lakume kasuwar waya a Kano
Kun ji cewa an tafka asarar dukiya da kadarori na biliyoyin Naira da gobara ta kama a kasuwar sayar da wayoyi watau Farm Centre a Kano.
Rahotanni sun tabbatar da cewa aƙalla shaguna 300 gobarar ta babbake da safiyar ranar babbar sallah, Juma'a 6 ga watan Yuni, 2025.
Shugaban kasuwar ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an yi asara mai ɗumbin yawa musamman a ɓangaren shagunan sayar da wayoyi da kayan gyara.
Asali: Legit.ng

