Kudirin Ƙirƙiro Ƙarin Jiha 1 a Arewacin Najeriya Ya Samu Gagarumin Goyon Baya a Majalisa

Kudirin Ƙirƙiro Ƙarin Jiha 1 a Arewacin Najeriya Ya Samu Gagarumin Goyon Baya a Majalisa

  • Kudirin kirkiro jihar Apa daga cikin jihar Benuwai ya fara samun goyon baya a Majalisar Wakilan Tarayya
  • Hon. Philip Agbese ya bayyana goyon bayansa ga shirin ƙirƙiro jihar, yana mai cewa hakan zai kawo karshen wariyar da ake nuna wa yankin
  • Ya ce duk da kirkiro jiha na da matuƙar wahala amma za su jajirce wajen tabbatar da sun cimma nasara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ɗan Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Hon. Philip Agbese, ya ce ƙirƙirar Jihar Apa daga cikin Jihar Benuwai zai taimaka wajen magance tsangwama da wariya da yankin ke fuskanta.

Hon. Agbese wanda ke wakiltar Ado/Ogbadigbo/Okpokwu a Majalisar Wakilai, ya kuma buƙaci a ƙirƙiri sababbin ƙananan hukumomi a jihar Benuwai.

Dan Majalisa daga Benue, Hon. Philip Agbese.
Dan Majalisar Tarayya ya goyi bayan kirkiro Jihar Apa a Arewacin Najeriya Hoto: @HonPhilipAgbese
Source: Twitter

Ɗan Majalisar ya bayyana haka ne da yake zantawada ƴan jarida ranar Laraba a Abuja, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamna Radda ya yi fallasa kan hadakar 'yan adawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa ake nemam kirkiro jihar Apa?

Ya ce wannan matakin zai ƙara kusantar da gwamnati ga jama'a, ya inganta ayyuka, da buɗe ƙofofin samun arziki a yankin.

A halin yanzu dai, majalisar dokokin tarayya na aiki kan gyaran kundin tsarin mulki na 1999, inda ta karɓi shawarwari da dama, ciki har da buƙatar ƙirƙirar sababbin jihohi.

“Ta hanyar ƙirƙiro ƙarin ƙananan hukumomi da Jihar Apa, za mu rage tazarar da ke tsakanin mutane da gwamnati, mu tabbatar da cewa sun samu kulawa da albarkatun da suka dace da su.
“Idan ƙananan hukumomi suka zama kusa da mutane, za a samu ingantaccen shugabanci. Jama’a za su fi samun damar ƙulla alaƙa da shugabanninsu, wanda hakan zai sa gwamnati ta rika yin abin da ya dace.”
“Jihar Apa za ta kawo ci gaba da bunƙasa yankinmu. Muna da albarkatun ɗan adam da na ƙasa, kuma da zarar an ƙirƙiro wannan jiha, za mu fito da baiwar mu."

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Jiga jigai 3 sun nemi ruguza haɗaƙar Atiku, Obi da yan haɗaka a ADC

- Hon. Philip Agbese.

Ya kara da cewa tarihi ya nuna yankin na fuskantar tsangwama wajen rabon albarkatu da ayyukan ci gaba.

Majalisar Wakilan Tarayya.
Hon. Philip Agbese ya bukaci sarakuna su shiga gwagwarmayar kirkiro jihar Apa Hoto: @NGRHouse
Source: Facebook

Wane kalubale ake fuskanta wajen ƙara jiha?

Agbese, wanda shi ne mataimakin kakakin Majalisar Wakilai ya amince cewa ƙirƙiro jihohi na da ƙalubale, amma ya ce abu ne mai yiwuwa idan aka jajirce da haɗin gwiwar jama’a.

“Mu yi amfani da wannan damar ta sake duba kundin tsarin mulki domin tsara makomar mu, mu tabbatar cewa mazabarmu ta samu kulawar da ta dace," in ji shi.

Agbese ya yi kira ga masu ruwa da tsaki, ciki har da shuwagabannin al’umma da sarakuna, da su mara wa kudirin ƙirƙiro Jihar Apa daga cikin Jihar Benuwe baya.

Majalisa na duba kudirorin samar da jihohi 46

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar wakilai na duba buƙatu kusan 46 na ƙirƙirar sababbin jihohi da 117 na ƙananan hukumomi a faɗin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta yi magana kan ƙera makamin nukiliya bayan yaƙin Iran da Isra'ila

Arewa ta Tsakiya ce ke kan gaba wajen neman ƙarin jihohi, yayin da Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu suka yi gaba wajen neman ƙarin ƙananan hukumomi.

Majalisar na kuma kan duba buƙatu biyu na daidaita iyakokin jihohi da kuma kusan kudurori 86 na sauya kundin tsarin mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262