Sowore: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Yi Tonon Silili kan Hadakar 'Yan Adawa

Sowore: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Yi Tonon Silili kan Hadakar 'Yan Adawa

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya taso jagororin haɗakar ƴan adawa a gaba
  • Omoyele Sowore ya bayyana cewa da yawa daga cikin mutanen da ke ciki haɗakar sun cutar da ƴan Najeriya
  • Ya nuna cewa jagororin haɗakar ba su da wani tarihin kirki kuma ba mutane ba ne masu daraja waɗanda zai iya tarayya da su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC a zaɓen 2023, Omoyele Sowore, ya ce ba zai iya yin aiki tare da ƴan siyasar da ke cikin haɗaka a ADC ba.

Omoyele Sowore ya ce ba zai yi aiki da su ba ne domin wasu daga cikinsu, ba su da tarihin kirki.

Sowore ya soki jagororin hadaka
Sowore ya ce 'yan hadaka sun cutar da 'yan Najeriya Hoto: @YeleSowore
Source: Facebook

Omoyele Sowore ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin 'The Morning Brief' na tashar Channels Tv a ranar Laraba, 9 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar haɗaka ADC ta zaɓi ɗan takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An samu bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Sowore ya ce kan ƴan haɗaka?

Sowore ya bayyana cewa ba zai iya zama da wasu daga cikin ƴan siyasar ADC ba, yana mai kiran su ƴan siyasa marasa tausayi da sanin yakamata.

"Akwai mutane da yawa cikin wannan haɗaka da ka ambata da ba zan iya zama da su a wuri guda ba, ina nufin a karan kaina, ba tare da na ji sha’awar yin abin da ba zai dace da halina ba. Wannan shi ne matsalar."
“Ba zan iya watsi da waɗannan abubuwan ba. Ba zan iya watsi da mutanen da ke cikin haɗaka da suka cutar da ƴan Najeriya ba, waɗanda suka aikata abin da za a kira da mugunta."
"Mutanen da muka sani ba su da tausayi, ba su da halin kirki, ba su da nagarta ko tarihi mai kyau."
“Babu wani sharaɗi da za a iya basu da zai sa su gyara halayensu, ko canja dabi’unsu, ko yadda suka saba rayuwa."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamna Radda ya yi fallasa kan hadakar 'yan adawa

"Su irin mutanen nan ne da rayuwarsu ta danganta da mugunta, cin hanci, zaluntar al’umma, da son kai. Don haka babu wani sharaɗi da zai iya canja su."

- Omoyele Sowore

Sowore ya yi magana kan hadakar 'yan adawa
Sowore ya soki hadakar 'yan adawa Hoto: @YeleSowore
Source: Twitter

Sowore ya ƙara da cewa sharaɗin da ke iya sa ya yi aiki da kowa shi ne idan mutumin na da niyyar taimaka wa ƴan Najeriya da kuma ceto ƙasar daga hannun jam’iyya mai mulki da kuma waɗanda ke ƙoƙarin komawa mulki ta hanyar sabuwar haɗaka.

Sowore ya soki gwamnonin Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC a zaɓen 2023, Omoyele Sowore, ya caccaki wasu daga cikin gwamnonin Arewa.

Omoyele Sowore ya soki gwamnonin ne saboda matakin da suka ɗauƙa na kulle makarantu a lokacin watan Ramadan.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya bayyana matakin da suka ɗauka a matsayin jahilci da wawanci, inda ya nuna cewa bai kamata addini ya kawo cikas ga karatu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng