Gwamnatin Bola Tinubu Ta ba Ganduje Mukami a FAAN, Ya Fara Aiki

Gwamnatin Bola Tinubu Ta ba Ganduje Mukami a FAAN, Ya Fara Aiki

  • An nada tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin shugaban gudanarwar hukumar FAAN
  • Abdullahi Ganduje ya samu mukamin ne kwanaki kadan bayan ya ajiye shugabancin jam’iyya mai mulki a Najeriya ta APC
  • Binciken Legit ya gano cewa hukumar FAAN na da alhakin kula da dukkan filayen jiragen saman da ke fadin Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bayan kwanaki kaɗan da saukarsa daga shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa, tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya samu sabon mukami daga gwamnatin tarayya.

An bayyana Ganduje a matsayin sabon shugaban gudanarwar hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya (FAAN) yayin da ake kaddamar da sababbin mambobin hukumar a Abuja.

An ba Ganduje mukami a hukumar FAAN
An ba Ganduje mukami a hukumar FAAN. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa minista mai lura da harkokin sufurin jiragen saman Najeriya, Festus Keyamo ne ya bayyana haka a yau.

Kara karanta wannan

APC: 'Yan siyasar Arewa sun fara neman kujerar Ganduje gadan gadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya samu mukami a gwamnatin Tinubu

Kamar yadda aka bayyana a wajen kaddamarwar, nadin Ganduje ya zo ne kwanaki bayan ya ajiye kujerarsa a matsayin shugaban jam’iyyar APC ta ƙasa saboda wasu dalilai.

Bayan saukar Ganduje, jam’iyyar APC ta zabi Ali Bukar Dalori a matsayin sabon shugaban riko na ƙasa domin ci gaba da jagorancin jam’iyyar.

Yayin da ake rade radin cewa Bola Tinubu zai iya watsi da Abdullahi Ganduje, ana ganin sabon mukami a FAAN ya kore jita jitar.

A yanzu haka dai ana zuba ido domin ganin ayyukan da Abdullahi Ganduje zai yi a ma'aikatar da makomar shi a siyasance.

Menene aikin hukumar FAAN a Najeriya?

Daily Post ta wallafa cewa hukumar FAAN na da alhakin kula da dukkanin filayen jiragen saman a Najeriya.

Ayyukan hukumar sun haɗa da tabbatar da tsaro, inganci da nagarta wajen tafiye-tafiye ta jiragen sama a fadin ƙasar.

FAAN tana lura da fasinjoji da kamfanonin jiragen sama, kana tana gudanar da harkokin da dama a filayen jirage domin ƙara samun ci gaba da bunkasa bangaren sufurin jiragen sama.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi magana a karon farko bayan Shugaba Tinubu ya ba shi muƙami a FAAN

Hukumar na taka muhimmiyar rawa wajen habaka harkokin sufurin sama a Najeriya, ta hanyar sanya ido kan gudanarwa da inganta ayyuka a dukkan filayen jiragen saman ƙasa.

Ministan sufurin jiragen saman Najeriya
Ministan sufurin jiragen saman Najeriya. Hoto: Festus Keyamo
Source: Facebook

Kallon yadda Ganduje zai taka rawa a FAAN

Nadin Ganduje a wannan sabuwar kujera na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran sake fasalin bangaren sufuri da harkokin jirgin sama a Najeriya.

Duk da cewa matsayin bai shafi siyasa kai tsaye ba, za a zuba ido domin ganin rawar da Ganduje zai taka a FAAN kasancewarsa wanda ya kware a harkokin siyasa.

Legit ta tattauna da Hamza Muhammad

Wani matashi dan APC a jihar Kano mai suna Hamza Muhammad ya ce har yanzu Ganduje ne jagoransu a siyasa.

Hamza ya ce:

"Duk da cewa kowa yana da ra'ayinsa, amma da ni ne zan koma gefe ne kawai ba tare da karbar wani mukami ba.
"Rashin mukami kuma ba ya nuna cewa ba Ganduje ba ne jagoran APC a jihar Kano. Za mu cigaba da masa biyayya."

Hadimin Ganduje ya gargadi Bola Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa wani hadimin tsohon shugaban APC na kasa, Aminu Dahiru ya nuna fushi kan shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Yadda jagororin APC suka ki tarbar Kashim Shettima a Kano bayan Ganduje ya yi murabus

Aminu Dahiru ya bayyana cewa shugaban kasa ya yi wa 'yan APC a Kano rauni har guda uku kuma akwai ranar ramuwa.

Ya kuma yi gargadi da cewa lokaci na zuwa da za a fahimci muhimmancin Abdullahi Ganduje a siyasar Kano da Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng