Wike Ya Bayar da Umarni kan Mabarata da Masu Sana’o’i da Suka Cika Titunan Abuja

Wike Ya Bayar da Umarni kan Mabarata da Masu Sana’o’i da Suka Cika Titunan Abuja

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya kaddamar da sabon shiri Abuja don kawar da dukkanin masu karamin karfi da bara daga birnin
  • An kafa kwamitin hadin gwiwa da jami’an tsaro don aiwatar da umarnin, inda za a rika zagayawa domin cafke wadanda ake zargi
  • A cewar Wike, wannan shiri ya biyo bayan bukatar da ake da shi na kawata Abuja a matsayin babban birnin kasar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ministan Babban Birnin Tarayya, Barista Nyesom Wike, ya bayar da umarni na gaggawa a kan masu karamin karfi a Abuja.

Ya bayar da umarnin korar mabarata, masu sana’o’i a kan titi, yan jari bola, da 'tsageru' daga cikin Abuja da garuruwan da ke kewaye da ita.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fitar da N7.7bn, zai siyo jiragen sama masu gano maɓoyar ƴan bindiga

Ministan Abuja, Nyesom Wike
Wike ya ba da umarni a kan mabarata a Abuja Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Lere Olayinka, mai ba Minista shawara na musamman kan harkokin yada labarai da kafafen sada zumunta ne ya sanar da haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya ba da umarni kan mabarata

Jaridar Leadership News ta wallafa cewa, an kaddamar da wani samame da aka sa wa suna ‘Operation Sweep Abuja.'

An kaddamar da shirin domin kwashe mabarata, masu yawon banza, masu sana’a a titi da 'yan jari bola, da mutanen da ake zargin da aikata laifuka da ta da zaune tsaye a Abuja.

Nyesom Wike zai fara korar mabarata daga Abuja
Wike na son a tsaftace Abuja Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Source: Twitter

Sanarwar ta ce:

“Daidai da dokar kariyar muhalli ta Abuja da sauran dokoki masu alaƙa, Ministan Abuja, Barrister Nyesom Wike, ya bayar da umarnin gaggawa domin korar dukkannin mabarata, masu sana’a a titi da masu binciken shara 'yan jari Bola daga babban birin.'
“Abin da ya dace shi ne babban birnin ƙasa ya kasance abin alfahari, ba wurin taruwar mabarata da masu tattara shara ba, domin yawancin su wakilan masu aikata miyagun laifuka ne.”

Kara karanta wannan

An tsinci gawar ministan sufuri awanni bayan shugaban kasa ya kore shi daga aiki a Rasha

Jami’ai za su bi umarnin Wike

Sanarwar ta ci gaba da cewa tuni aka samar da hadin gwiwar jami’an tsaro da hukumomin Abuja domin ganin cewa an aiwatar da umarnin kamar yadda Wike ya bayar.

A cewar Lere Olayinka:

“Domin cimma wannan buri da aka sa a gaba, an tura jami'an hadin gwiwar jami’an tsaro da hukumomin Abuja domin cafke duk wanda aka samu yana bara, tattara shara, yawon banza ko wata dabi’ar da ke kawo barazana ga zaman lafiyar mazauna birnin.”
“An kuma shirya tsarin tantance su, tare da miƙa su ga gwamnatocin jihohin da suka fito.”

Dalilin Wike na karbar Ministan Abuja

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da ya sa ya yarda ya kasance cikin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Wike ya bayyana cewa ya shiga gwamnatin ce domin ya bada gudunmawa wajen ganin an samu ci gaba da ribar dimokuraɗiyya ga ‘yan Najeriya baki daya.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani bikin godiya bisa kammala wasu ayyuka da gwamnatin sa ta FCT ta aiwatar da kuma ƙaddamar da Asokoro, Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng