2027: Peter Obi Ya Ziyarci Sheikh Rigachikun a Kaduna, Malam Ya Masa Kyauta

2027: Peter Obi Ya Ziyarci Sheikh Rigachikun a Kaduna, Malam Ya Masa Kyauta

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, ya kai ziyara wajen Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun a Rigachikun, jihar Kaduna
  • Sanarwa daga shafin Sheikh Rigachikun ta bayyana cewa an tarbi Obi cikin girmamawa, inda aka ba shi kyautar babban riga da hula ta gargajiya
  • A cikin hotunan da aka yada, an hango fitattun mutane ciki har da Sheikh Alkali Abubakar Salihu daga Zaria da wasu manyan mutane

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Yayin da yan siyasa ke fara shirye-shiryen zaben shekarar 2027, sun fara ziyarce-ziyarce.

Dan takarar shugaban kasa a 2023 karkashin LP, Peter Obi ya kai ziyara gun babban malami a jihar Kaduna.

Peter Obi ya ziyarci Sheikh a Kaduna
Peter Obi ya gana da Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun. Hoto: Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da shafin Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya wallafa a yau Laraba 9 ga watan Yulin 2025 a manhajar Facebook.

Kara karanta wannan

2027: ADC a Kudancin Najeriya ta fadi matsayarta kan tsayar da Atiku takara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jiga-jigan ADC da ake zargin suna neman takara

Hakan na zuwa ne yayin da manyan yan siyasa ke ta shirin yin haɗaka domin kwace mulkin Bola Tinubu a zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Daga cikin manyan jiga-jigan adawa a Najeriya da ke cikin tafiyar sun hada da Peter Obi da Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi da sauransu.

Ana ta jita-jita kan dan takarar da ADC ta haɗaka za ta tsayar domin karawa da Tinubu a zaɓen saboda abin da suke zargi gwamnatin ta gaza kawo karshen matsalolin Najeriya.

Tun farko Peter Obi da ke gaba-gaba a masu neman takara ya mika bukatar cewa shi wa'adi daya kacal zai yi idan aka ba shi damar takara da kuma bayan ya lashe zaben.

Peter Obi ya ziyarci Sheikh Rigachikun a Kaduna
Peter Obi ya gana da Sheikh Rigachikun a Kaduna. Hoto: Peter Obi.
Source: Twitter

Obi ya ziyarci Yusuf Sambo Rigachikun a Kaduna

A cikin sanarwar, an ce Obi ya ziyarci malamin ne a gidansa da ke Rigachikum a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana cikin rigima tsakanin masoyan Sarki da Aminu Ado, Sanusi II ya bar Najeriya

Sanarwar ta ce:

"Alhamdulilah.
"A safiyar yau Laraba, tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Mr. Peter Obi ya ziyarci Sheikh a gidansa da ke Rigachikun Kaduna.
"Alhamdulillah, muna godiya da karamci.

Majiyoyi sun ce yayin ziyarar, Sheikh Rigachikun ya ba Peter Obi kyautar babban riga ta Hausawa da hula inda ya nuna jin dadi kan ziyarar da jigon adawar ya kai masa a gidansa.

A cikin hotunan da aka yada, an gano manyan mutane da dama da suka kasance a dakin da aka yi zaman a Kaduna.

Daga cikin wadanda za a iya gani akwai Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria da sauran manyan mutane.

Peter Obi ya yi magana kan Arewacin Najeriya

Mun ba ku labarin cewa dan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi ya faɗi tanadin da ya yi wa yankin Arewacin Najeriya.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa yankin Arewa zai amfana idan ya zama shugaban ƙasa.

Peter Obi ya bayyana cewa yana da shiri kan hanyar magance matsalolin rashin tsaro da suka daɗe suna ci wa yankin tuwo a ƙwarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.