Ana Maganar Hadaka, Dangote Ya Rubutawa Bola Tinubu Budaddiyar Wasika

Ana Maganar Hadaka, Dangote Ya Rubutawa Bola Tinubu Budaddiyar Wasika

  • Alhaji Aliko Dangote ya jinjinawa shugaba Bola Tinubu kan jagorancinsa wajen inganta abubuwan more rayuwa da shawo kan ambaliya
  • Dangote ya ce aikin Bar Beach da sababbin titunan da ake yi sun nuna hangen nesa da jajircewar gwamnatin shugabab Bola Tinubu
  • Ya ce gidauniyar sa na shirin tallafa wa yankunan da ambaliya ke shafa ta hanyar samar da kudin da zai taimaka wajen farfado da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya bayyana godiya da yabo ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan matakan da ya ɗauka don habaka ayyukan raya kasa.

Alhaji Aliko Dangote ya yaba da kokarin Bola Tinubu wajen rage barazanar ambaliya, musamman a yankin Bar Beach da ke Legas.

Kara karanta wannan

Bayan zargin badakala, Peter Obi ya fadi alakar da ta hada shi da Abacha

Dangote ya yaba da kokarin shugaba Tinubu
Dangote ya yaba da kokarin shugaba Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Dangote ya bayyana hakan ne a cikin wata budaddiyar wasika da ya aike wa shugaban kasar, kamar yadda hadimin Bola Tinubu, Sunday Dare ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jaddada cewa sababbin titunan tarayya da ake ginawa a fadin kasa, na daga cikin manyan nasarorin gwamnatin Tinubu.

Dangote ya ce Tinubu na da hangen nesa

Dangote ya kwatanta Tinubu da jagora mai hangen nesa, musamman kan yadda ya fara aikin gyaran Bar Beach wanda ke kare yankin Victoria da ke Legas daga ambaliyar ruwa.

Dangote ya ce:

“Wannan aiki na Eko Atlantic, wanda yanzu ke ya kai fadin fili har hekta 1,000 kuma yana da tsawon kilomita 8.5, ya dakile ambaliya a yankin.
"Wannan nasara ita ce ta saka al’ummar yankin Victoria suka huta da tashin hankali na ambaliyar ruwa.”

Punch ta wallafa cewa Dangote ya kara da cewa:

“Shugabanci irin naka ya kawo ƙarshen ambaliyar da ke addabar tituna kamar titin Ahmadu Bello, titin Akin Adesola da sauransu.”

Kara karanta wannan

Katsina: Biki ya koma makoki bayan bindige ɗan shekara 10, an harbi budurwa a kwankwaso

Dangote ya yaba wa Tinubu kan gina tituna

Dangote ya ci gaba da cewa Tinubu ya nuna karfin gwiwa da kishin kasa ta hanyar farfado da manyan ayyuka kamar titin gabar tekun Lagos zuwa Calabar da kuma titin Sokoto zuwa Badagry.

Ya bayyana titin Sokoto-Badagry a matsayin wani gagarumin aiki da aka bari har tsawon shekaru 48, yana mai cewa kamfanin Hitech ke jagorantar aikin bisa kwarewa da sahihanci.

Lokacin da Bola Tinubu ya ziyarci matatar Dangote.
Lokacin da Bola Tinubu ya ziyarci matatar Dangote. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Dangote zai ba da tallafin ambaliya

Dangote ya bayyana cewa kamfaninsa ya miƙa ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon ambaliya a Amurka, yana mai jan hankalin duniya kan illar sauyin yanayi.

Ya kuma sanar da cewa gidauniyarsa na shirin samar da asusun taimako ga yankunan da ambaliya ke shafa a Najeriya, domin rage haduran da ke fuskantar al’umma.

Dangote ya rage kudin mai a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa matatar Dangote ta sanar da rage kudin litar man fetur a fadin Najeriya zuwa N820.

Kara karanta wannan

'Zuwansa alheri ne': Ribadu ya faɗi yadda Tinubu ya ceto Najeriya daga tarwatsewa

An bayyana cewa Dangote ya rage kudin litar man fetur ne sakamakon saukar kudin danyen mai a kasuwar duniya.

Masana harkokin man fetur sun bayyana cewa alamu sun nuna cewa za a cigaba da samun saukin farashin man fetur a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng