Dangote Zai Daina Sayo Mai daga Amurka, Fetur Zai Yi Araha a Najeriya daga Disamba
- Matatar Dangote za ta dakatar da shigo da danyen mai daga kasashen waje nan da Disamba 2025, za ta koma dogaro da man cikin gida
- Wannan mataki zai rage matsin lamba kan Naira, saboda rage buƙatar kuɗin musaya da kuma iya sa farashin man ya sauka a cikin Najeriya
- Matatar na da burin ƙarfafa dogaro kan kai a fannin makamashi, ta yadda Najeriya za ta daina shigo da man fetur da aka sarrafa daga waje
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas – Matatar man Dangote na shirin dakatar da shigo da danyen man fetur nan da Disamba 2025, wanda zai kawo karshen shigo da dubunnan gangunan mai daga waje.
Mataimakin shugaban kamfanin Dangote, Devakumar Edwin, wanda ke kula da matatar man da ke Legas, ya ce daga Disamba matatar za ta rika samar da danyen man nata daga cikin gida Najeriya.

Source: UGC
Dangote zai daina shigo da mai daga waje
Rahoton Bloomberg ya nakalto Devakumar Edwin yana cewa matatar ta shigo da danyen mai daga ƙasashen Brazil, Angola, Ghana, Equatorial Guinea, da ma Amurka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, Devakumar Edwin ya ce:
“Ingantacciyar dangantaka tsakanin matatar, ƴan kasuwar mai na gida, da gwamnati zai haifar da wadatar danyen man Najeriya a kai a kai.”
Rahoton ya lura cewa matatar ta karɓi kusan rabin danyen man fetur nata a watan Yuni daga masu samar da shi na gida, waɗanda za su iya samar da ƙari ga matatar yayin da kwangilolin samar da man na ƙasashen waje za su ƙare nan ba da jimawa ba.
Idan aka aiwatar da hakan, matakin zai sa matatar ta dogara gaba ɗaya kan danyen man Najeriya a madadin man da take shigowa da shi daga waje.
Tasirin matakin Dangote ga tattalin Najeriya
Bayanai da aka tattara sun nuna cewa matatar ta samar da kashi 53% na danyen man fetur nata daga masu samar da shi na cikin gida yayin da ta sayo kashi 47% daga Amurka a watan Yuni.
Matatar a halin yanzu tana sarrafa ganga 550,000 na danyen mai a kowace rana, a cewar Devakumar Edwin.
An shirya Dangote zai karɓi jiragen ruwa biyar dauke da danyen mai daga kamfanin NNPVL a watan Yuli, a cewar bayan jerin rarraba mai da aka gani.
Idan Matatar Dangote ta dakatar da shigo da danyen mai nan da Disamba 2025 kuma ta dogara gaba ɗaya kan danyen man Najeriya, akwai yiwuwar hakan zai iya shafar tattalin arzikin Najeriya.
Legit Hausa ta tattaro wasu hanyoyi uku da matakin dangote zai shafi tattalin Najeriya:
1. Rage matsin lambar musayar kudin waje
Dakatar da shigo da danyen mai zai iya ceto Najeriya daga matsin lambar musayar kudin ƙasashen waje masu yawa, saboda shigo da danyen mai, musamman daga Amurka, wanda ke karawa Dala karfi a kan Naira.
A watan Yunin 2025, kashi 47% na danyen mai na matatar Dangote ya fito ne daga Amurka, wanda ya ci biliyoyin daloli kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sauyawa zuwa danyen mai na gida zai iya rage wannan buƙatu, mai yiwuwa zai daidaita darajar Naira, wadda ta raunana zuwa kusan N1,600/$1 kan dala saboda ƙarancin kuɗin musayar.

Source: Getty Images
2. Fadurwar farashin fetur a gida
Shirin gwamnatin Najeriya na sayarwa Dangote danyen mai da Naira maimakon Dala, ya riga ya haifar da raguwar farashin fetur.
Idan aka aiwatar da shirin gaba ɗaya sakamakon daina shigo da mai daga waje da Dangote zai yi, wannan zai iya ƙara rage farashin man fetur na cikin gida daga Disamba.
Hakazalika, hakan zai rage hauhawar farashi da kuma rage tsadar rayuwa, kamar yadda farashin man fetur ke shafar farashin sufuri da kayayyaki.
3. Ƙara dogaro da kai a fannin tattalin arziki
Ta hanyar samar da dukkanin danyen mai a cikin gida, matatar Dangote ta yi daidai da burinta na asali na kawo ƙarshen dogaron Najeriya kan shigo da mai da aka sarrafa daga waje.
Daina shigo da danyen man zai iya ƙarfafa 'yancin kai na makamashi na Najeriya da kuma rage fuskantar hauhawar farashin mai a duniya.
Matatar Dangote ta rage farashin man fetur
Tun da fari, mun ruwaito cewa, matatar man Dangote ta sanar da rage farashin litar fetur daga N840 zuwa N820, biyo bayan saukar farashin danyen mai a kasuwar duniya.
Wannan mataki na Dangote ya sa sauran kamfanonin man fetur da ke hulda da ita sun bi sahun ta wajen rage farashin domin ci gaba da fafatawa a kasuwa.
Saukar farashin man fetur na zuwa ne bayan karewar yaƙin da aka gwabza tsakanin Isra’ila da Iran na tsawon kwanaki 12 wanda ya jawo tsadar farashin danyen man.
Asali: Legit.ng



