Harin da Aka Kai Fadar Sarki Muhammdu Sanusi II Ya Ƙara Tayar da Ƙura a Jihar Kano

Harin da Aka Kai Fadar Sarki Muhammdu Sanusi II Ya Ƙara Tayar da Ƙura a Jihar Kano

  • Kungiyoyin fararen hula watau CSOs sun buƙaci ƴan sanda su fito su yiwa al'imma bayani kan harin da aka kai Fadar Sarkin Kano
  • A cewar ƙungiyoyin, sun samu labarin magoya bayan Aminu Ado ne suka yi ɓarna a Fadar Ƙofar Kudu da Muhammadu Sanusi II ke zaune
  • Wannan lamari na ci gaba da tayar da ƙura a tsakanin mutanen Kano sakamakon yadda aka jikkata mutane da lalata motocin ƴan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Kungiyoyin al'ummar da ke zaune a Kano sun fara nuna damuwa kan harin da wasu tsageru suka kai fadar Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.

Ƙungiyoyin fararen hula a Kano sun ce shirun da rundunar ƴan sanda ta yi kan lamarin, duk da an san wanda ya jawo, babban abin takaici ne.

Kara karanta wannan

Ana cikin rigima tsakanin masoyan Sarki da Aminu Ado, Sanusi II ya bar Najeriya

Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II.
Kungiyoyin fararen hula.sun buƙaci ƴan sanda sun kamo duk mao hannu a harin Fadar Sarkin Kano Hoto: Masarautar Kano
Source: Facebook

Leadership ta ce gamayyar kungiyoyin fararen hula (CSOs) ƙarƙashin 'One Kano Agenda' ta nemi karin bayani daga ’yan sanda kan harin da aka kai wa Fadar Sarki ta Ƙofar Kudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kai hari Fadar Sarkin Kano na 16

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin magoya bayan Sarki na 15, Aminu Ado Bayero da kai hari Fadar da Sanusi II ke zaune a ranar Lahadi da ta gabata.

Lamarin ya faru ne a lokacin da Aminu Ado ke dawowa daga gidan marigayi attajirin Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, inda ya je ta’aziyya.

Motocin ƴan sanda babura da wasu kayayyaki sun lalace a harin, sannan kuma an jikkata wasu mutanen gari.

Harin Fadar Sanusi ya ja hankalin ƙungiyoyi

Kungiyoyin fararen hula sun yi tir da harin, inda suka buƙaci ƴan sanda su fito su bayyana wa al'umma gaskiyar abin da ya faru, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kungiyoyin da suka haɗu suka yi martani kan lamarin sun haɗa da Kano Digital Media Rangers, Youth Mobilisation by Media, Northern Youth Assembly, One Voice Development Initiative da da Beyond Border Alliance, Kano First Forum.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun fara kame bayan jina jina tsakanin masoyan Sanusi II da Aminu Ado

Sun ce bayanin da suka samu, Aminu Ado Bayero ya kauce wa hanyar da ya saba bi zuwa gidansa da ke Mandawari, ya zabi wucewa ta Kabara, gaban fadar Sarkin Kano.

Su wa suka kai hari fadar Sarkin Kano?

“Saboda haka, ana zargin wasu daga cikin ƴan rakiyarsa ne suka farmaki fadar Sanusi II.
"Wannan abu na iya jefa jihar Kano cikin rudani da rashin tabbas, kuma hakan na iya zama wani yunkuri da wasu marasa kishin ƙasa suka shirya da gangan don tayar da tarzoma,” in ji su.
Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero.
Kungiyoyin fararen hula.sun aika sako ga ƴan sanda kan ɓarnar da aka yi a Fadar Sarkin Kano Hoto: @HRHBayero
Source: Facebook

CSOs ɗin sun bukaci ’yan sanda su dauki mataki cikin gaggawa, inda suka ƙara da cewa:

“Don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Kano, muna kira ga rundunar ’yan sanda da ta gaggauta fara bincike kan harin da aka kai, wanda aka lalata kadarorin gwamnati, cin zarafin jami’an tsaro da fararen hula.

Sannan sun bukaci a gano, a kama tare da gurfanar da duk masu hannu a harin a. gaban ƙuliya.

Gwamnatin Kano ta yi magana kan harin fada

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta bayyana ɓacin ranta kan rikicin da ya auku a Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Gwamnatin Kano ta fito ta fayyace abin da ya faru a Fadar Sanusi II

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Garba Waiya, ya bayyana cewa tuni aka samu nasarar dawo da zaman lafiya a yankin.

Waiya ya nuna rashin jin daɗinsa bisa gazawar jami’an tsaro da ke gadin fadar wajen hana aukuwar hakan duk da cewa suna tsaye a wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262