Ana cikin Rigima tsakanin Masoyan Sarki da Aminu Ado, Sanusi II Ya Bar Najeriya
- Sarki Muhammadu Sanusi II ya bar Najeriya zuwa Afrika ta Kudu domin halartar taro yayin da ake rikici a Kano
- Shafin Masarautar Kano ta fitar da sanarwa tana cewa Sarki da Galadiman Kano sun isa Cape Town domin taron gudanarwa
- A ranar Lahadi, an samu artabu tsakanin masoya Sarki Sanusi da Aminu Ado Bayero, lamarin da ya jawo asarar rayuka a jihar Kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bar kasar Najeriya yayin da ake ta fama da rikicin masarauta a jihar.
An ce Sarkin ya isa kasar Afrika ta Kudu domin gudanar da wani taro mai muhimmanci a kasar.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa ta shafin Masarautar Kano ta wallafa a manhajar X a yau Talata 8 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya ɗauko Mai Martaba Sarkin Lafiya, ya ba shi shirgegen muƙami a Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ke faruwa a Kano tsakanin sarakuna 2
Wannan na zuwa ne yayin da ake tsaka da bincike kan abubuwan da suka jawo rigima tsakanin magoya bayan sarakunan guda biyu.
A ranar Lahadi 6 ga watan Yulin 2025 wasu magoya bayan Aminu Ado Bayero suka yi artabu da masoyan Sarki Sanusi II wanda ya jawo asarar duniyoyi.
Rundunar yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce kafa kwamitin bincike domin tabbatar da gano masu hannu a rikicin.
Yan sanda sun kama mutane 4 a Kano
Daga bisani, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a rikicin da ya faru a fadar Sarkin Kano da ke unguwar Kofar Kudu.
Kakakin yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata 8 ga watan Yulin 2025.
Kiyawa ya ce:
“Eh, rundunar ta kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a lamarin, kuma suna tsare a hannun ƴan sanda yayin da ake cigaba da bincike.”

Source: Facebook
Musabbabin barin Sanusi II, Galadiman Kano Najeriya
Sanarwar ta ce Sarki Muhammadu Sanusi II ya isa kasar Afrika ta Kudu a yau Talata domin halartar taron.
Sanusi II ya isa kasar ne da Galadiman Kano, Malam Munir Sanusi domin taron gudanarwa na kamfanin MTN.
Za a gudanar da taron ne a birnin Cape Town da ke kasar Afrika ta Kudu da ke Kudancin Nahiyar Afrika.
Sanarwar ta ce:
"Mai Martaba Khalifa Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano, tare da Malam Munir Sanusi, Galadiman Kano, suna halartar taron hukumar gudanarwar MTN na duniya a birnin Cape Town, Afrika ta Kudu."
An kori masoyan Aminu Ado daga fadar Sanusi
A baya, kun ji cewa masu biyayya ga Aminu Ado Bayero sun fuskanci matsala daga fada, saboda rashin goyon bayan Sarki Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan
Rikicin sarauta: Gwamnatin Kano ta fito ta fayyace abin da ya faru a Fadar Sanusi II
Wasu jami’an fada da iyalansu sun sha ruwan ihu yayin da aka zargi ’yan daba da balle rufin gidajensu domin tilasta musu ficewa.
Rikicin masarautar Kano na cigaba da jefa masu rike da mukaman gargajiya cikin rudani kan wanda za su mara wa baya.
Asali: Legit.ng
