Gwamna Radda Ya Fadi wani Sirri kan 'Yan Bindigan da Suka Addabi Katsina
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya taɓo batun matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
- Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa ƴan bindigan da suke addabar jihar, suna rayuwa ne a cikin al'umma
- Gwamnan ya nuna cewa gwamnatinsa ta duƙufa wajen ɗaukar matakan ganin ta magance matsalar rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi magana kan ƴan bindigan da suka addabi jihar.
Gwamna Radda ya bayyana cewa kusan kaso 90% cikin 100% na ƴan bindigan da ke addabar jihar ba baƙi ba ne kuma ba ƴan waje ba ne.

Source: Facebook
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a ranar Talata a shirin 'Sunrise Daily' na tashar Channels Tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Radda ya ce kan matsalar ƴan bindiga?
Dikko Radda ya ce matsalar rashin tsaro ta kasance babban cikas ga ci gaban da ake buƙata a jihar Katsina.
Ya ce ko da yake gwamnonin jihohi suna matsayin shugabannin tsaro a jihohinsu, sojoji da ƴan sanda suna aiki ne bisa cin gashin kansu.
Gwamnan ya bayyana cewa domin ƙarfafa matakan tsaro, gwamnatinsa ta ƙirƙiri wata rundunar matasa ta cikin gida, wadda aka samo daga yankunan da suka fi fama da hare-haren ƴan bindiga.
"Waɗannan samari sun fi sanin yadda yankin ya ke, kuma sun fi sanin waɗanda ke aikata ta’addancin."
“Yawancin waɗanda ke aikata ta’addanci a cikin mu suke. Ba wasu baƙi ba ne. Kaso 90% da wani abu cikin 100% daga cikinsu mun san iyayensu, har da kakanninsu. Kuma suna rayuwa a cikinmu."
- Gwamna Dikko Radda
Gwamna Radda na ƙoƙarin magance rashin tsaro
Gwamna Radda ya sake jaddada muhimmancin shigar da al’ummomi cikin yaƙi da ƴan bindiga.

Source: Facebook
“Wannan yanayin na buƙatar haɗin kai da sanya mutanen da ke a matakin ƙasa, shi ya sa muka kafa wannan runduna, domin mutanen gari su riƙa samar da bayanai."
“Za su iya jagorantar farmaki zuwa maboyar ƴan bindigan domin sun san yankin sosai. Za su iya gano masu ba da bayanai ga ƴan bindiga da kuma masu tallafa musu da kayan aiki da abinci."
"Idan ba a warware wannan matsala daga tushe ba, to ba za a iya magance matsalar tsaro yadda ya kamata ba."
- Gwamna Dikko Radda
Karanta wasu labarai kan ƴan bindiga
- 'Yan sanda da 'yan bindiga sun gwabza kazamin fada a jihohi 3, an kwato mutane 29
- 'Yan bindiga sun kwace ikon karamar hukuma a Katsina? 'Yan sanda sun yi bayani
- An shiga tashin hankali a Katsina, ƴan bindiga sun 'ƙwace ikon' karamar hukuma
Ƴan bindiga sun sace basarake a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma.
Ƴan bindigan waɗanda suka kai hari a cikin dare, sun farmaki wani ƙauye da ke cikin ƙaramar hukumar Matazu ta jihar.
Maharan sun yi awon gaba da Hakimin Karaduwa, Alhaji Abdullahi Bello, a yayin harin da suka kai a cikin dare.
Asali: Legit.ng

