Rikicin Sarauta: Gwamnatin Kano Ta Fito Ta Yi Fayyace Abin da Ya Faru a Fadar Sanusi II

Rikicin Sarauta: Gwamnatin Kano Ta Fito Ta Yi Fayyace Abin da Ya Faru a Fadar Sanusi II

  • Gwamnatin Kano ta bayyana ɓacin ranta kan rikicin da ya auku a Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Ibrahim Garba Waiya ya ce gwamnati ba ta jin daɗin abin da ya faru ba duk da akwai jami'an tsaro a wurin
  • Ya ce wasu mutane da ba ruwansu a faɗan sun samu raunuka amma an yi nasarar dawo da zaman lafiya a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - A ranar Lahadi da ta gabata ne aka farmaki fadar mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da ke Ƙofar Kudu.

Lamarin ya jawo lalata ɗaya daga cikin ƙofofin fadar da fasa motocin ƴan sanda da ke gadin wurin, duk da an ce lokacin Sarki Sanusi II ba ya nan.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi magana kan rigimar da ta faru a fadarsa da Aminu Ado ya zo wucewa

Gwamnatin Kani ta nuna damuwa kan abin da ya faru a fadar Sarki Sanusi II.
Rigimar da aka yi a kusa da Fadar Muhammadu Sanusi ta jawo hankalin gwamnatin Kano Hoto: @kyusufabba, @hrhbayero
Source: Twitter

Masarautar Kano ta zargi magoya bayan Sarki na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda ya wuce ta gaban fadar, kamar yadda Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rikici ya kaure a Fadar Sarkin Kano

Legit Hausa ta tattaro cewa magoya bayan sarakunan Kano, Sanusi II da Aminu Ado sun ɓarke da rigima a lokacin da Aminu Ado zai wuce ta gaban fadar.

Sai dai wani ganau, Muktar Dahiru, ya ce ba magoya bayan Aminu Bayero ne suka kai hari fadar Sanusi II ba, sai dai rigima ta haɗa su da wasu ƴan daba a wurin.

A cewarsa, rikicin ya fara ne bayan da ‘yan daba suka fara ɗaga makamai tare da toshe hanya domin hana Sarkin na 15 wucewa ta Kofar Kudu da suka hango tawagarsa.

Ya ƙara da cewa hakan da suka yi ne ya jawo martani daga dayan bangaren, lamarin da ya sa ’yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa su, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kano: Ƴan sanda sun fara binciken rikicin magoya bayan Sanusi II da Aminu Ado Bayero

Ya ce Aminu Ado Bayero da tawagarsa sun fito ne daga unguwar Koki, inda suka je ziyarar ta’aziyya gidan Alhaji Aminu Dantata, sai suka ci karo da ‘yan daba da suka toshe hanya.

Gwamnatin Kano ta yi takaicin abin da ya faru

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana faruwar lamarin a matsayin abin takaici, inda ta ce wasu mutane da babu ruwansu sun ji rauni a lokacin harin.

Gwamnatin ta nuna damuwa da yadda harin ya faru duk da akwai jami’an tsaro jibge a fadar Mai Martaba Sanusi II.

Gwamma Abba Kabir Yusufa na Kano.
Gwamnatin Abba ta ce an kwantar da tarzomar da ta faru a faɗar Sarkin Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Twitter

Da yake zantawa da ƴan jarida, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Garba Waiya, ya bayyana cewa tuni aka samu nasarar dawo da zaman lafiya.

“Wasu mutane kalilan sun ji rauni a lokacin wannan rikici, amma babu wanda ya rasa ransa.
"Wannan ci gaba ya damu gwamnatin jihar, amma muna kira ga Kanawa da su kwantar da hankali kuma su kasance masu zaman lafiya a koda yaushe,” in ji Waiya.

Waiya ya nuna rashin jin daɗinsa bisa gazawar jami’an tsaro da ke gadin fadar wajen hana aukuwar hakan duk da cewa suna tsaye a bakin ƙofar shiga.

Kara karanta wannan

Rashin biyayya: An umarci masoyan Aminu Ado su fice daga gidan Sarki Sanusi II

Masarautar Kano ta yi martani kan rikicin

A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II , ya zargi magoya bayan Alhaji Aminu Ado Bayero, da kai hari a fadarsa.

A cikin wata sanarwa da masarautar Kano ta fitar, ta ce Sanusi II ba ya cikin fadar a lokacin da lamarin ya auku rananr Lahadi.

Ta ce wannan ba shi ne karon farko da Aminu ke wucewa da gangan ta kofar fadar ba, yana mai cewa yana yi ne domin tsoratar da jama’ar unguwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262