An Gwanza Fada a Filato, an Kashe 'Yan Banga 70 da Kona Gidaje
- Akalla 'yan banga 70 ne suka rasa rayukansu a harin kwantan bauna da ‘yan bindiga suka kai a kananan hukumomin Kanam da Wase
- Shugaban masu sa-kai na Kukawa ya ce an birne sama da mutane 60, kuma ana ci gaba da gano gawarwaki a dazuka da gonaki
- Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun kona gidaje a Bunyun, inda suka kashe karin masu sa-kai 10 da ke tsaron al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato – Rahotanni sun nuna cewa sama da masu sa-kai 70 ne suka mutu a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a kusa da kauyukan Kukawa da Bunyun da ke yankin Kanam da Wase.
Lamarin ya afku ne da misalin karfe 2 na rana a ranar Litinin, lokacin da masu sa-kai daga karamar hukumar Wase suka nufi maboyar ‘yan bindiga.

Source: Original
Leadership ta wallafa cewa sai dai kafin su isa, ‘yan bindigar sun musu kwantan bauna a dajin Madam, wanda ke tsakanin jihohin Filato, Bauchi da Taraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da kashe 'yan banga a Filato
Daily Trust ta wallafa cewa shugaban kungiyar masu sa-kai na Kukawa, Aliyu Baffa, ya shaida cewa fiye da gawarwaki 70 ne aka gano bayan harin.
A cewar shi:
“A Kukawa kadai mun birne fiye da mutum 60. Wasu gawarwaki har yanzu suna cikin daji da gonaki,”
Ya kara da cewa harin ya faru a wajen da bai wuce nisan kilomita daya kacal daga garin Kukawa ba, yayin da ‘yan sa-kai ke kokarin shiga dajin Madam da ke cike da ‘yan bindiga.
Wadanda suka tsira bayan harin Filato
Shugaban ya bayyana cewa wasu daga cikin masu sa-kai sun tsira daga harin, suna masu cewa sun sha kashi sosai daga ‘yan bindigar da suka fi su yawan makamai.
“Wadanda suka tsira sun ce sai da suka nemi mafaka a cikin daji. Ba karamin hari aka kai mana ba,”
In ji shi.
Har yanzu ana ci gaba da nemowa da gano sauran gawarwaki da ake zargin na cikin dajin ko gonakin da ke yankin.

Source: Twitter
An kona gidaje a Bunyun, karin mutane sun mutu
Wani mazaunin kauyen Bunyun da ke gundumar Nyalun a karamar hukumar Wase, Musa Ibrahim ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki a yankin.
A cewarsa:
“Sun kashe masu sa-kai 10 da ke aikin tsaro a Bunyun, sannan sun kona gidaje da dama a yankin.”
An kama dan ta'adda a jihar Filato
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kama wani mutumin da ake zargi da tare hanya domin kai hari wa matafiya a jihar Filato.
Rahotanni sun bayyana cewa mutumin da aka kama mai suna Stephen Gyang dauke da bindiga samfurin AK47 kirar gida.
Jami'an tsaro na cigaba da bincike domin gano sauran mutanen da Gyang ke aiki tare da su wajen kai farmaki kan matafiya a Filato.
Asali: Legit.ng

