Olubadan: Babban Basarake a Najeriya Ya Rasu Yana da Shekara 90

Olubadan: Babban Basarake a Najeriya Ya Rasu Yana da Shekara 90

  • An shiga jimami a jihar Oyo biyo bayan rasuwar ɗaya daga cikin manyan sarakunan da ake tunƙaho da su
  • Mai martaba Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin ya koma ga mahaliccinsa watanni bayan ya hau kan karagar mulki
  • Oba Owolabi Olakulehin ya yi bankwana da duniya ne kwanaki biyu bayan ya cika shekara 90 da haihuwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Mai Martaba Olubadan na Ibadanland, Oba Owolabi Olakulehin, ya rasu bayan watanni a kan karagar mulki.

Sarkin wanda ya hau karagar mulki a watan Yuli na shekarar 2024, ya rasu da safiyar Litinin, 7 ga Yuli, 2025.

Olubadan na Ibadan ya rasu
Oba Owolabi Olakulehin ya yi bankwana da duniya Hoto: Oyo Insights
Source: Twitter

Jaridar Tribune ta rahoto cewa rasuwarsa na zuwa ne bayan shekara guda da hawa kujerar sarauta.

Babban basarake a Oyo ya rasu

Rasuwar Oba Olakulehin, wanda aka haifa a ranar 5 ga Yuli, 1935, ta zo ne kasa da kwana biyu bayan ya cika shekaru 90 da haihuwa.

Kara karanta wannan

Oba Olakulehin: Babban basarake a Najeriya da ya rasu kwana 3 da cika shekaru 90

Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ne ya miƙa masa sandar mulki a ranar 12 ga Yuli, 2024, inda ya zama Olubadan na Ibadanland na 43 a tarihi.

Oba Olakulehin ya hau sarauta ne daga matsayin Balogun Olubadan, bayan rasuwar Oba (Dr.) Moshood Lekan Balogun, Alli Okunmade II, wanda ya rasu yana da shekaru 81 a duniya a ranar 14 ga watan Maris, 2024.

Wani majiɓinci na kusa da majalisar masarautar ya tabbatar da rasuwar sarkin ga jaridar The Punch.

"Mun samu saƙon cewa Mai martaba Sarki ya rasu da safiyar nan. Ya rasu inda zai haɗu da magabatansa. Duk da dole ne a jira gwamnatin jiha ta sanar da hakan a hukumance."

- Wata majiya

Wata majiya ma daga fadar masarautar ta tabbatar da labarin rasuwar basaraken.

Majiyar ta bayyana cewa Otun Olubadan, Oba Rashidi Ladoja, wanda shi ne ke biye da marigayin wajen hawa sarautar Olubadan, yana ƙasar waje a halin yanzu, amma ana sa ran dawowarsa gida nan ba da jimawa ba.

“Muna sa ran dawowar tsohon gwamnan jihar Oyo kuma Otun Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, wanda a yanzu yana ƙasar waje, zuwa gida."

Kara karanta wannan

Yobe: Hadimin gwamna ya yi murabus, ya faɗi dalilansa na shiga jam'iyyar ADC

"Lallai an riga an sanar da shi labarin."

- Wata majiya

Wanene Oba Owolabi Olakulehin?

Owolabi Olakulehin ya fito ne daga ƙaramar hukumar Ibadan ta Arewa maso Gabas a jihar Oyo.

Asalinsa yana da nasaba da dangin Okugbaja da ke unguwar Ita Baale a cikin garin Ibadan.

Olubadan na Ibadan ya yi bankwana da duniya
Oba Owolabi Olakulehin ya koma ga mahaliccinsa Hoto: Seyi Makinde
Source: Twitter

Marigayi Owolabi Olakulehin da magabacinsa duk sun fito ne daga ƙaramar hukumar Ibadan ta Arewa maso Gabas.

Olakulehin yana da tarihin aikin soja, inda ya yi aiki a rundunar sojojin Najeriya (NA).

A shekarar 1992, a lokacin Jamhuriyya ta uku karkashin jam’iyyar SDP, Olakulehin ya shiga siyasa, inda ya samu nasarar lashe kujera a majalisar wakilai.

Olubadan ya gargaɗi Sarkin Hausawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, ya aika saƙon gargaɗi ga sarkin Hausawa na Sasa.

Basaraken ya bayyana cewa a bisa tsarin doka, ba a san da shi ba a matsayin ɗaya daga cikin wakilansa.

Hakan dai na zuwa ne bayan an yi naɗin Alhaji Ahmeɗ Ciroma a matsayin sarkin Hausawan Sasa ba tare da amincewar Olubadan ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng