A Karo na Biyu, An Ƙara Ɗaga Jana'izar Fitaccen Ɗan Kasuwa, Alhaji Aminu Ɗantata a Madina
- A karo na biyu, an sake ɗaga jana'izar marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga bayan sallar La'asar zuwa bayan Magriba a masallacin Madina
- Makusantan marigayin sun bayyana cewa gawar ta isa Madina da safiyar yau Talata, 1 ga watan Yuli kuma za a masa jana'iza da Magriba
- Tuni dai tawagar gwamnatin tarayya da ta Kano da wasu manyan jiga-jigai suka isa Madina domin halartar jana'izar Ɗantata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Madina - A karo na biyu cikin sa'o'i 24, an ɗaga jana'izar fitaccen ɗan kasuwar nan mai taimakon al'umma, Alhaji Aminu Ɗantata a Saudiyya.
Rahotanni daga makusantan marigayin sun ce an mayar da jana'izar zuwa bayan sallar Magriba, maimakon La'asar da aka tsara a farko.

Source: Twitter
An maida jana'izar Ɗantata zuwa Magriba
Jaridar Aminiya ta kawo rahoton cewa za a yi wa Aminu Ɗantata jana'iza a masallacin Annabi SAW da ke Madinah bayan sallar Magriba yau Talata, 1 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan
Allahu Akbar: Yadda aka yi jana'izar Aminu Ɗantata a masallacin Annabi SAW a Madina
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Mustapha Junaid, wanda ya kasance mataimaki na musamman ga marigayin, ya bayyana cewa gawar Alhaji Aminu Ɗantata ta isa Madina.
Ya ƙara da cewa bayan isowar gawar filin jirgin sama an tafi da ita zuwa Shakzura domin kammala shirye-shirye na ƙarshe kafin gudanar da jana’iza.
“AlhamdulilLah an ɗauki marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga filin jirgi na Madina, yanzu haka an nufi Shakzura domin kammala shirye-shirye.
"Daga bisani za a kai shi Haramin Madina domin yi masa jana’iza, kamar yadda hukumomin Saudiyya suka amince,” in ji Junaid.
Abin da ya jawo jinƙirin jana'izar Ɗantata
Wannan ne karo na biyu da aka samu sauyin lokacin jana’iza tun bayan rasuwar Marigayi Aminu Ɗantata.
Da farko an sanar cewa za a yi jana’izar ne a ranar Litinin, amma daga bisani aka ɗaga zuwa yau Talata kamar yadda Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana.

Source: Facebook
Ministan ya bayyana cewa an dage jana’izar ne saboda gawar ba ta isa Madina a kan lokaci ba, kuma akwai wasu matakai da hukumomin Saudiyya suka gindaya kafin a gudanar da jana’iza a ƙasarsu.
“Gwamnatin Saudiyya tana da ƙa’idoji da sharudda game da shigowa da gawarwaki domin yi musu jana’iza a ƙasar. Saboda haka yanzu ana cikin cike-ciken takardu tsakanin Saudiyya da iyalan marigayin,” in ji Idris.
Sai dai a halin yanzu, bayan cika dukan sharuɗɗa da ƙa'idoji, makusantan marigayi Ɗantata sun sanar da cewa za a yi jana'izar bayan Magriba a haramin Madina.
Tawagar Kano ta ziyarci iyalan Ɗantata a Madina
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf da tawagar Kano sun kao ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a Madina.
Gwamna ya ziyarci gidan marigayin ne tare da wata tawaga da ta hada.da sarkin Kano na 16, mai martaba Muhammadu Sanusi II.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da shirye shiryen yi wa marigayin jana'iza a masallacin Annabi SAW da ke birnin Madina a Saudiyya.
Asali: Legit.ng
