Yadda Yan Bindiga Ke Tilastawa Fursunoni Alaƙanta Kansu da Gwamna Dauda a Zamfara
- Bayan kashe Yellow Danbokolo, 'yan bindiga sun tilasta wa wasu fursunoni cewa su ‘yan uwan Gwamna Dauda Lawal ne domin karɓar fansa
- Bidiyon ya nuna yadda fursunonin suke amsa tambayoyin yan bindiga da cewa daga Kucheri suka fito kuma suna da alaƙa da gwamnan Zamfara
- Gwamnatin Zamfara ta karyata ikirarin, ta ce yan bindigar bindigar na amfani da fursunoni wajen yaɗa ƙarya da ƙara wa kansu ƙarfin guiwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Bayan ragargazar da sojoji da yan sa kai suka yi wa ‘yan bindiga a yankin Zamfara, maharan sun koma amfani da dabarar yaɗa ƙarya da barazana.
Daga cikin dabarun akwai tilasta wa fursunoni da suka kama su fadi cewa su ‘yan uwan manyan jami’an gwamnati ne domin karɓar fansa.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Fada ya barke tsakanin wasu 'yan gida 1 a Filato, an yi kisan kai

Source: Twitter
Yadda yan bindiga ke tilastawa fursunoni a Zamfara
Wani daga cikin fursunonin da ke cikin bidiyon da ya karade intanet ya fadi cewa shi dan uwan Gwamna Dauda Lawal ne, cewar Premium Times.
Bidiyon farko ya nuna su biyu suna sanye da riga mai ruwan kasa da kore, suna fadin sun fito daga Kucheri kuma suna da masana'anta.
A cikin bidiyon na biyu, an tilasta wa daya daga cikinsu ya fadi cewa shi da Gwamna Dauda daga uwa daya da uba daya suke.
Yan bindigar sun ce idan ba a biya kudin fansa ba, za su kashe su, kuma ya nemi a kira gwamna Dauda domin ya tara kudin.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa wanda ke cikin bidiyon ba ‘dan uwan gwamnan Zamfara ba ne.

Source: Original
Gwamnatin Zamfara ta musanta ikirarin yan bindiga
Mai magana da yawun Gwamna Dauda, Sulaiman Bala Idris, ya ce gwamnan mace daya ce kadai ‘yar uwarsa.
Bala Idris ya bayyana cewa wannan sabon salon yaƙi ne da ‘yan bindigar ke kokarin amfani da shi domin haifar da tashin hankali.
Ya kara da cewa an ga yadda fursunonin ke cikin tsoro da firgici a bidiyon, wanda ke nuna sun faɗi hakan ne bisa tsoron hallaka.
Gwamnatin Zamfara ta karyata ikirarin, ta ce yan bindigar bindigar na amfani da fursunoni wajen yaɗa ƙarya da ƙara wa kansu ƙarfi.
Gwamnatin ta ce tana daukar matakan ceto waɗanda aka kama tare da mayar da su hannun iyalansu cikin lafiya.
An bukaci jama'a da su yi hattara da irin waɗannan bidiyo domin ka da su fada cikin yaɗa labaran ƙarya da ke ƙarfafa ‘yan ta’adda.
Ana zargin Bello Turji na neman sulhu
Mun ba ku labarin cewa majiyoyi sun bayyana cewa Bello Turji yana neman a yi sulhu bayan mutuwar dan uwansa kuma kwamandansa.
An ce Turji na shirin ganawa da wasu kungiyoyin 'yan bindiga domin duba yiwuwar mika wuya ga gwamnatocin jihohin Arewa maso Yamma.
Wata majiya ta ce, Turji ba ya da karfi yanzu, Kachalla Danbokolo ne ke tafiyar da ayyukan fada da kayayyaki a daji wanda ake ganin mutuwarsa za ta rage karfin dan ta'addan.
Asali: Legit.ng
