Yadda Dangote Ya Raka Gawar Dantata daga Dubai zuwa Madina
- Attajirin Afirka, Aliko Dangote ya raka gawar kawunsa, Alhaji Aminu Dantata, daga Abu Dhabi zuwa Madina
- Za a yi sallar jana’iza a masallacin Annabi Muhammad SAW bayan sallar la’asar a yammacin yau Talata
- Alhaji Aminu Dantata ya rasu a ranar Asabar, kuma ya bukaci a birne shi a birnin Madina cikin wasiyyar da ya yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Shahararren attajiri kuma dan kasuwa mafi arziki a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya dauki nauyin raka gawar kawunsa, Alhaji Aminu Alhassan Dantata zuwa Madina.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an dauko gawar Dantata ne daga Abu Dhabi zuwa birnin Madina domin jana’iza da birne shi.

Source: Facebook
Sanusi Dantata ne ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ce Dangote da kansa ya halarci jigilar gawar zuwa ƙasar Saudiyya.

Kara karanta wannan
Allahu Akbar: Yadda aka yi jana'izar Aminu Ɗantata a masallacin Annabi SAW a Madina
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar da cewa gawar ta isa Madina safiyar Talata, kuma za a gudanar da sallar jana’iza a masallacin Annabi SAW bayan sallar la’asar, ƙarfe 1:30 na rana agogon Najeriya.
Menene dalilin birne Dantata a Madina?
Alhaji Aminu Dantata, ɗan kasuwa kuma jigo Najeriya, ya rasu ne a ranar Asabar a Abu Dhabi yana da shekaru 94, kuma ya bayyana cikin wasiyyarsa cewa a birne shi a Madina.
Bayan cikarsa, iyalansa da na kusa suka nemi izinin gwamnatin Saudiyya domin cika wannan wasiyya.
Sai da aka shafe lokaci ana bin wasu ka’idoji kafin gwamnati ta amince da a birne shi a birnin mai tsarki.

Source: Twitter
Da farko, an shirya gudanar da jana’izar ne a ranar Litinin, amma daga baya aka dage ta zuwa Talata domin kammala shirye-shiryen da suka wajaba.
Za a yi jana’izar Dantata a masallacin Annabi
Rahotanni sun nuna cewa za a yi sallar jana’iza a masallacin Annabi da ke Madina, kuma za a birne shi a makabartar Baqi'a, inda fitattun sahabbai da malamai suka huta.

Kara karanta wannan
A karo na 2, an ƙara ɗaga jana'izar fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Ɗantata a Madina
Sanusi Dantata ya bayyana cewa Dangote na cikin dawainiyar tafiyar da zuciya ɗaya, wanda hakan wata alama ce ta girmamawa da soyayya ga wanda ya yi masa uwa da uba.
Ya yi addu’ar Allah ya ji kan sa, ya kuma dawo da iyalai da abokan arziki lafiya daga tafiyar zuwa Saudi domin halartar jana’izar.
Ana cigaba da jimamin mutuwar Dantata
Alhaji Aminu Dantata ya bar babban gibi a kasuwanci a Najeriya, musamman a Arewacin ƙasar inda ya kasance fitaccen mai taimakon jama’a da gina harkokin ci gaban al’umma.
Jana’izarsa ta ja hankalin mutane da dama daga ciki da wajen Najeriya, ciki har da manyan 'yan siyasa, attajirai da malamai da ke nuna alhini da addu’a a gare shi.
Dantata ya bar wa Aminu Ado wasiyya
A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, mai martaba Aminu Ado Bayero ya isa Madina jana'izar Dantata.
Sarkin ya bayyana cewa hakan na cikin wasiyyar da marigayin ya masa ta yin tarayya cikin masa sutura da jana'iza.
A daya bangaren, gwamna Abba Kabir Yusuf ya hada tawagar gwamnatin Kano da ta hada da Muhammadu Sanusi II zuwa Madina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng