An Shirya Gudanar da Jana'izar Alhaji Aminu Dantata bayan La'asar a Madina

An Shirya Gudanar da Jana'izar Alhaji Aminu Dantata bayan La'asar a Madina

  • Tuni aka kammala shirin gudanar da jana'izar attajirin dan kasuwar Najeriya, Alhaji Aminu Dantata a birnin Madina a ranar Talata
  • An tabbatar da cewa jana’izar za ta gudana ne a Masallacin Harami na birnin Madina, wanda shi ne mafi tsarki ga Musulmi bayan na Makka
  • Birne attajirin a birnin Madina na daya daga cikin yunkurin da yan uwansa ke yi na cika masa burin da ya dade yana fatan ya cimma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Zuwa an jima kada, bayan sallar la'asar za a gudanar da jana’izar fitaccen ɗan kasuwa kuma attajirin Najeriya, Alhaji Aminu Dantata.

Makusantansa sun tabbatar da cewa za a gudanar da jana'izar n, a Masallacin Harami da ke birnin Madina a kasar Saudiyya.

Kara karanta wannan

A karo na 2, an ƙara ɗaga jana'izar fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Ɗantata a Madina

Marigayi Alhaji Aminu Dantata
Za a birne Alhaji Aminu Dantata a Saudiyya Hoto: @SasDantata/X
Source: Twitter

A hira da ya yi da BBC Hausa, Alhaji Mustapha Junaidu, wanda shi ne mataimaki na musamman ga marigayin, ya bayyana cewa duk wani shiri an kammala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a gudanar da jana’izar Aminu Dantata

Rahotanni sun nuna cewa an karɓo gawar marigayin daga Dubai, inda ya rasu, sannan aka isar da ita zuwa Madina tare da wasu daga cikin 'yan uwansa.

A hirar da ya yi, Alhaji Mustapha Junaidu ya ce:

"Alhamdu lillah, an karɓi marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga filin jirgi na Madina, yanzu haka za a kai shi Shakzura inda ake yin shiri na ƙarshe kafin daga bisani a kai shi Harami domin sallar jana’iza kamar yadda Saudiyya ta amince.”

Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar, yana da shekara 94 a shekarar Miladiyya, da kuma shekara 97 a kalandar Hijira, bayan fama da jinya a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Ana shirin cika wasiyyar Alhaji Aminu Dantata

Kara karanta wannan

Dantata: Dangote ya karbi tawagar gwamnatin Kano da Jigawa a Madina

Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin ya kasance yana yawan addu’a cewa Allah Ya karɓi rayuwarsa a Madina, birnin da Annabi Muhammad (SAW) ya rayu da sahabbansa.

Wannan dalili ya sanya iyalansa da makusanta nema izini daga hukumomin Saudiyya domin a yi masa suttura a can, kuma suka amince.

Tuni dai tawagar gwamnatin tarayya da ta haɗa da manyan jami’an gwamnati da malamai ta isa Madina domin halartar jana’izar.

Za a cika burin Alhaji Aminu Dantata
Za a gudanar da jana'izar Alhaji Aminu Dantata bayan sallar la'asar Hoto: @SasDantata/X
Source: Twitter

Tawagar na ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, wanda kuma tsohon Gwamnan Jigawa ne.

Sauran mambobin tawagar sun hada da Lateef Fagbemi SAN, Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati, Alhaji Mohammed Idris, Ministan Yaɗa Labarai, fitaccen malami a Najeriya, Sheikh Aminu Daurawa da sauransu.

Saudiyya ta amince a birne Aminu Dantata

A baya, mun wallafa cewa hukumomin kasar Saudiyya sun bayar da izinin birne gawar Alhaji Aminu Alhassan Dantata, fitaccen ɗan kasuwa a Najeriya.

Za a gudanar da birne marigayin ne da sanyin safiyar Talata, 1 ga watan Yuli, 2025, a Masallacin Annabi (Masjid an-Nabawi), da ke birnin Madinah.

Wannan ne cikar buri da marigayi ya yi na kwanciya kusa da kabarin matarsa, Rabi'a, wacce ta rasu a shekarar 2023, kuma yanzu haka ana shirin cika masa burin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng