Dantata: Ganduje, Barau da Jiga Jigan APC Sun Dura a Madinah domin Halartar Jana'iza

Dantata: Ganduje, Barau da Jiga Jigan APC Sun Dura a Madinah domin Halartar Jana'iza

  • Ɗage jana'izar fitaccen dan kasuwa kuma attajiri, Alhaji Aminu Dantata ya ba wasu fitattu a Najeriya damar halarta
  • Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin da Abdullahi Ganduje sun tashi daga Abuja zuwa Madina domin jana’izar marigayin
  • Barau ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da misalin karfe 9:00 na daren jiya Litinin 30 ga watan Yunin 2025

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Manyan yan siyasa da masu rike da madafun iko daga Najeriya sun cika Madina domin halartar jana'izar marigayi Aminu Dantata.

Hakan ya biyo bayan mutuwar attajiri, Alhaji Aminu Dantata wanda ya rasu a Abu Dhabi, kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a karshen mako.

Barau da Ganduje sun isa Madinah domin jana'izar Dantata
Abdullahi Ganduje da Barau sun dura a Madinah domin halartar jana'izar marigayi Aminu Dantata. Hoto: Sanata Barau I Jibrin.
Source: Twitter

Wannan na cikin wata sanarwa da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a jiya Litinin 30 ga watan Yunin 2025 a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

A karo na 2, an ƙara ɗaga jana'izar fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Ɗantata a Madina

Musabbabin ɗage jana'izar Dantata zuwa Talata

Hakan ya biyo bayan ɗage jana'izar marigayi Alhaji Aminu Ɗantata zuwa yau Talata, 1 ga watan Yuli, 2025 a ƙasar Saudiyya.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan bayan tawagar gwamnatin Najeriya ta isa Madina .

Ya ce an samu wannan tsaiko ne sakamakon rashin isowar gawar marigayin a kan lokaci, wanda ya faru saboda ƙa'idojin da Saudiyya ta shimfiɗa.

Dantata: Barau da Ganduje sun dura a Madinah

Sanarwar ta ce mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibrin na daga cikin wadanda suka isa Madina.

Har ila yau, tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, shi ma a isa birnin Madina domin halartar jana'izar.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Barau da Ganduje sun tashi daga Abuja zuwa Madina a kasar Saudiya, a daren Litinin 30 ga watan Yunin 2025.

Kara karanta wannan

Dantata: Dangote ya karbi tawagar gwamnatin Kano da Jigawa a Madina

Za a yi jana’izar dattijon a yau Talata 1 ga watan Yulin 2025 bayan fasa gudanar da jana'izar a jiya Litinin saboda wasu dalilai.

Barau da Ganduje sun dura a Madinah domin jana'izar Dantata
Sanata Barau da Ganduje sun samu isa Madinah domin jana'izar Dantata. Hoto: Ismail Mudashir.
Source: Facebook

Dantata: Jiga-jigan yan siyasa da suka isa Madinah

An ce Sanata Barau ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da misalin karfe 9:00 na daren jiya Litinin.

Sauran wadanda suka tafi sun hada da Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, Sanata Muntari Dandutse da Hon Ali Madaki na Majalisar Wakilai.

Har ila yau, akwai Hon Hamisu Ibrahim Chidari daga Mazabar Makoda/Dambatta, Ahmad Munzali Dantata (ɗan marigayin), Usman Yahaya Kansila da Hon. Sani Bala da sauransu.

Dantata: Wakilan Tinubu da malamai sun isa Madinah

A baya, kun ji cewa wata tawaga daga Gwamnatin Tarayya ta isa birnin Madinah a Saudiyya domin jana'izar fitaccen attajiri, Alhaji Aminu Dantata.

Marigayin, Aminu Alhassan Dantata ya rasu ne a ranar Asabar 28 ga watan Yunin 2025 a Abu Dhabi, kasar Hadaddiyar Daular Larabawa yana da shekaru 94.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an shirya gudanar da jana’izarsa a Madinah a jiya Litinin kafin dagewa zuwa yau Talata 1 ga watan Yulin 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.