Jirgin Kamfanin Rano Air Ya Gamu da Matsala bayan Ya Tashi daga Kano zuwa Sakkwato

Jirgin Kamfanin Rano Air Ya Gamu da Matsala bayan Ya Tashi daga Kano zuwa Sakkwato

  • Jirgin kamfanin Rano Air ya gamu da matsalar inji bayan ya taso daga Kano zuwa Sakkwato, lamarin da ya jawo ya yi saukar gaggawa
  • Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama (NCAA) ta dakatar da tashin jirgin mai lamba 5N-BZY har sai an kammala bincike
  • NCAA ta jaddada cewa ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da cewa kowane jirgin sama yana bin ƙa'idoji da dokokin sufuri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta bayar da umarnin dakatar da tashi jirgin Rano Air mai lambar rajista 5N-BZY a Sakkwato.

Wannan mataki ya biyo bayan wani lamari da ya faru yayin tafiyar jirgin daga Kano zuwa Sakkwato, inda aka ruwaito cewa injinsa ya samu matsala a sararin samaniya.

Kara karanta wannan

An kashe jagoran 'yan banga, Saleh Fiya Fiya a dajin Kaduna

Jirgin kamfanin Rano Air ya samu matsala bayan tashi daga Abuja zuwa Katsina.
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da tashin jirgin Rano Air a Abuja Hoto: Rano Air
Source: UGC

Daily Trust ta tattaro cewa NCAA ta yanke wannan hukunci ne domin tabbatar da bin ka’idoji da tsari kan duka kamfanonin jiragen sama da ke aiki a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya faru da jirgin Rano Air a Abuja

An gano cewa injin jirgin saman na farko (engine 1) ya samu matsala yayin da jirgin ke tsaka da tafiya bayan ya bari Kano, da nufin zuwa Sakkwato.

Bayanai sun nuna cewa hayaki ya tashi a cikin ɗakin fasinjoji da kuma wajen matuƙan jirgin, sakamakon haka, ma’aikatan suka kunna na'urar rufe hanci da bayar da iska.

Daga nan kuma kuma matuƙan jirgi suka ɗauki mataki tare da saukar gaggawa domin kaucewa abin da ka iya faruwa sakamakon ɓacin injin a filin jirgin Sokoto.

Wata majiya ta bayyana cewa hayakin da ya tashi a cikkn jirgin ya gushe kafin ya gama sauka, kuma ya sauka lafiya ba tare da wata matsala ba, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Taraba: Mummunan hatsari ya faru a cikin kasuwa bayan motar yashi ta markaɗe mutane

Wannan lamari ya haifar da tsaiko a jadawalin zirga-zirgar jiragen kamfanin Rano Air, inda wasu fasinjojin da ke shirin tafiya daga Sokoto zuwa wasu wuraren suka samu jinkiri.

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo.
Jirgin Rano Air ya sauka a Sokoto duk da matsalar inji da ya samu bayan ya baro Kano Hoto: @Keyamo
Source: Twitter

Wane mataki mahukunta suka ɗauka?

A cikin rahoton da kakakin NCAA, Michael Achimugu ya fitar, ya ce hukumar ta dakatar da amfani da jirgin har sai an kammala cikakken bincike kan lafiyarsa.

“Injiniyoyi suna duba jirgin a halin yanzu domin gano musabbabin matsalar injin da kuma fitowar hayaki,” in ji shi.

A halin da ake ciki, NCAA ta jaddada cewa ba za ta sassauta ka’idojin tsaro na sufurin jirgin sama ba, ko da kuwa hakan na iya haifar da tsaiko a ayyukan jirage.

NCAA ta taɓa dakatar da kamfanin Max Air

A baya, kun ji cewa hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ta dakatar da ayyukan jiragen Max Air na tsawon watanni uku.

Hukumar NCAA dai ta ɗauki wannan matakin ne bayan jirgin kamfanin Max Air ya gamu da hatsari, inda tayarsa ta fashe a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma.

Duk da cewa dukkan fasinjoji 53 da ke cikin jirgin sun tsira ba tare da wani rauni ba, an dakatar da amfani da jiragen kamfanin Max Air na tsawon wata uku.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262