An Ɗage Jana'izar Fitaccen Ɗan Kasuwa, Aminu Ɗantata saboda Ƴar Matsala a Madina
- An ɗaga jana'izar marigayi Alhaji Aminu Ɗantata zuwa ranar Talata, 1 ga watan Yuli, 2025 a ƙasar Saudiyya
- Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan bayan tawagar gwamnatin Najeriya ta isa Madina
- Ya ce an samu wannan tsaiko ne sakamakon rashin isowar gawar marigayin a kan lokaci, wanda ya faru saboda ƙa'idojin da Saudiyya ta shimfiɗa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudi Arabia - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da cewa an ɗage jana’izar fitaccen ɗan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Aminu Dantata a Madina.

Kara karanta wannan
Zargin kisan kiristoci: Ɗan majalisar Amurka ya fashe da kuka yayin zama game da Najeriya
Aminu Ɗantata, ya rasu a ranar Asabar a Abu Dhabi, babban birnin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), bayan fama da jinya.

Source: Twitter
An ɗage jana'izar Aminu Ɗantata zuwa Talata
Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan ga BBC Hausa, yana mai cewa an ɗaga jana'izar zuwa gobe Talata a Madina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce akwai wasu ƙa’idoji da Saudiyya ta shimfiɗa dangane da shigar da gawa cikin ƙasar don yi mata jana’iza, wanda hakan ya kawo jinkirin kai gawar marigayin a kan lokaci.
Ministan ya tabbatar da cewa yanzu haka ana ci gaba da cike-ciken takardu tsakanin iyalan mamacin da hukumomin Saudiyya.
Abin da ya jawo jinkiri a jana'izar Ɗantata
“Da zarar an kammala cike-ciken, za a ɗauko gawar daga UAE zuwa Saudiyya,” in ji Muhammed Idris.
Ya ƙara da cewa ofishin Jakadancin Najeriya da ke Saudiyya da iyalan marigayin sun riga sun kammala duk wasu shirye-shiryen jana’iza, da zarar izini ya samu.
An ce Marigayi Aminu Dantata ya bar wasiyyar cewa a birne shi a Madina, birnin Manzon Allah (SAW), kuma Allah ya sa Saudiyya ta amince da hakan.
Tuni dai tawagar Najeriya ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ta isa birnin Madina domin halartar jana’izar.

Source: Facebook
Tawagar gwamnatin Najeriya ta isa Madina
Ƴan tawagar sun kunshi, Antoni Janar na ƙasa kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi (SAN), ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris da ƙaramin ministan harkokin gidaje, Yusuf Abdullahi Ata.
Haka kuma fitattun malaman addinin musulunci, Sheikh Aminu Daurawa, Dr Bashir Aliyu Umar, da Khalifa Abdullahi Muhammad na cikin tawagar.
Bugu da ƙari, Gwamna Abba Kabir Yusuf da takwaransa na jihar Jigawa, Umar Namadi sun jagoranci ta su tawagar domin halartar jana'izar Ɗantata a Madina
Daga cikin tawagar akwai Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, tsohon gwamnan Jigawa, Barista Ali Sa’ad Birnin Kudu, da wasu fitattun dattawan Kano.
Sakamakon tsaikon da aka samu wajen cika ƙa'idojin Saudiyya, an ɗaga jana'izar Ɗantata zuwa gobe Talata, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Aminu Ɗantata
A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar Alhaji Aminu Ɗantata, yana mai cewa wannan babban rashi ne ga ƙasa.

Kara karanta wannan
Trump: Gwamnati ta 'dora alhakin karuwar ta'addanci a Najeriya a kan shugaban Amurka
Tinubu ya yabawa gudummuwar da marigayin ya bayar wajen bunƙasa tattalin arzikin kasa da kuma taimakon jama'a.
Shugaban kasar ya ce Dantata ba wai kawai babban ɗan kasuwa ba ne, dattijo ne da ya kasance ginshikin zaman lafiya da cigaba a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
