Sojojin Najeriya Sun Kashe 'Yan ISWAP da ke Kokarin Dasa Bama Bamai a Borno
- Sojojin Najeriya sun kashe wasu daga cikin mayakan ISWAP da suka yi yunkurin dasa bama-bamai a hanyar Trans-Timbuktu, jihar Borno
- Majiyar tsaro ta bayyana cewa sai da aka fafata da yan bindigar, inda bayan sun ji ruwan wuta, wasu daga cikinsu suka tsere
- An kwato bindigu AK-47, babur, da kayan hada bama-bamai, tare da kayan da ake amfani da su wajen huda hanya domin boye bama-bamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Dakarun sojin Najeriya na Operation Hadin Kai, sun kashe wasu da ake zargin mayakan ISWAP a jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya afku ne yayin da mutanen biyu ke ƙoƙarin dasa bama-bamai a hanyar a jihar Borno.

Source: Twitter
Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Litinin, ya kara da cewa lamarin ya faru ne a gefen hanyar Trans-Timbuktu (TT) da ke nufin yankin Katarko–Goniri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun samu sahihan bayanai kan ISWAP
Majiyoyi daga rundunar sojin sun bayyana cewa wannan aikin ya biyo bayan sahihan bayanan leken asiri da suka nuna cewa wani rukuni na 'yan ta’adda na kokarin dasa bama-bamai a hanyar.
Majiyar ta ce:
“A yayin fafatawar, sojojin sun yi musayar wuta da ‘yan ta’addan na dan kankanin lokaci, inda suka kashe guda biyu, sauran kuma suka tsere.”
An kwato kayan makamai da dama daga wajen su da suka hada da bindigogun AK-47 guda biyu, bindiga magsinoni, babur, da kayan hada bam, da kuma wasu na’urori da ake amfani da su wajen huda hanya domin boye bama-bamai.
Dakarun Sojoji sun matsawa 'yan ta’adda
Rundunar sojin ta ce an ƙara himma wajen dakile dukkanin hanyoyin da yan ta'adda suka saba kai hare-hare da kuma kare fararen hula da dakarun soji.

Source: Facebook
Majiyar tsaro ta ce:
“Martani cikin gaggawa da sojojin suka yi ya hana wani mummunan hari da ‘yan ta’adda ke kokarin kaiwa kan motoci da sojoji da fararen hula ke amfani da su."

Kara karanta wannan
'An firgita su,' Mazauna Zamfara sun fadi halin da ake ciki bayan kisan dan uwan Turji
Wannan nasara ta zo ne a daidai lokacin da dakarun Najeriya ke cigaba da samun galaba a kan ‘yan ta’adda a wasu sassa na jihohin Zamfara da Sakkwato, inda ake ci gaba da kai farmaki da kame masu tayar da kayar baya.
'Yan ta'adda sun kashe dan sa-kai
A baya, kun samu labarin cewa makiyaya da ke zaune a cikin filin kiwo na Yardoka da ke ƙaramar hukumar Kubau suka kashe shugaban hukumar tsaron KADVIS, Saleh Shuaibu,
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da jami’an gwamnatin jihar Kaduna suka kai ziyarar aiwatar da umarnin kwace filin kiwo domin mika shi ga wani kamfani mai zaman kansa.
Majiyoyi sun ce jami’an gwamnati sun je wajen da hadin guiwar ‘yan sanda da DSS, domin aiwatar da tsarin mallakar sama da hekta 200 na fili ga kamfanin da gwamnati ta amince da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
