Gwamnonin Kudu Maso Gabas Sun Yiwa PDP Barazana ana Fama da Rikicin Cikin Gida

Gwamnonin Kudu Maso Gabas Sun Yiwa PDP Barazana ana Fama da Rikicin Cikin Gida

  • Gwamnan Enugu, Peter Mbah ya gargaɗi cewa yankinsa zai sake duba kasancewarsa a PDP idan bukatar da suka mika ba
  • Masu ruwa da tsaki a Kudu maso Gabas na son a tabbatar da Sunday Udeh-Okoye a matsayin sakataren jam’iyya na kasa
  • Sun yi barazanar cewa rashin mutunta wannan bukata za ta iya jawo wa PDP gagarumar asara ta jiga-jigai a shiyyar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Enugu – Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya ce yankin Kudu maso Gabas na da cikakken ‘yancin sake duba kasancewarsa a PDP idan har jam’iyyar ta gaza gyara matsalolinta.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron shugabannin zartaswar PDP na yankin da aka gudanar a Enugu, inda suka amince da Sunday Udeh-Okoye a matsayin sakataren jam’iyya na kasa.

Kara karanta wannan

2027: Matasan APC sun bullo da dabarar rakitowa Tinubu kuri'a miliyan 10

Ambasada Umar Iliya Damagum da Peter Mbah
Gwamnonin Kudu Maso Gabas gargadi shugabancin PDP Hoto: Amb Umar Iliya Damagum/Peter Ndabuisi Mbah
Source: Facebook

The Cable ta ruwaito cewa sanarwar da shugaban PDP na shiyyar, Ali Odefa, ya rattaba wa hannu, ta ce yankin zai sake nazari kan dangantakarsa da jam’iyyar idan aka hana su fitar da sakataren jam’iyyar na kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin PDP a Kudu maso gabas sun fusata

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa PDP ta Kudu maso Gabas ta bukaci kwamitin aiki na kasa (NWC) da ya girmama matsayarsu na ranar 29 ga Afrilu, wanda ya amince da Udeh-Okoye.

Sun kuma nemi jam’iyyar ta bar mukaddashin sakatare ya ci gaba da rike mukamin har sai an nada wanda kowa da kowa zai aminta da shi.

Gwamnan Enugu, Peter Mbah
Gwamnonin Kudu Maso Gabas za su iya barin PDP Hoto: Peter Ndubuisi Mbah
Source: Twitter

Da yake magana da manema labarai bayan ganawar sirri a gidan gwamnati na Enugu a ranar Lahadi, Gwamna Mbah ya yi gargaɗi cewa yankin na iya ficewa daga jam’iyyar.

Ya ce matsayin da kwamitin NWC, kwamitin amintattu na kasa (BoT) da shugabannin PDP na yankin Kudu maso Gabas (ZEC) suka dauka kan rikicin jam’iyyar ke fusata masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

'Ganduje ya jawo wa Kano abin kunya,' NNPP ta yi magana kan komawar Kwankwaso APC

Gwamnonin PDP sun goyi bayan NEC

Mbah ya kuma bayyana goyon bayansa ga babban taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga Yuni, 2025.

Duk da haka, ya ce har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, amma ya gaji da rikice-rikicen da suka mayar da jam’iyyar kamar wasan kwaikwayo.

Ya ce:

"Har yanzu ni dan PDP ne. Amma Kudu maso Gabas, da ni kai na, na da 'yancin sake duba kasancewarmu a jam’iyyar idan har PDP ta kasa daidaita kanta.”

Fitattun shugabanni da suka halarci taron sun hada da gwamnan Oyo, Seyi Makinde, shugaban BoT na PDP, Adolphus Wabara, Shugaban PDP na Kudu maso Gabas Ali Odefa da sauransu.

Sabuwar rigima ta kunno kai a PDP

A baya, mun wallafa cewa kwamitin amintattu na PDP ya bayyana rashin jin daɗi da matakan da muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Umar Damagum, ya ɗauka kan Samuel Anyanwu.

Kara karanta wannan

Rigimar APC: Ganduje ya yi murabus daga kujerarsa ta shugabancin jam'iyyar

Kwamitin ya bayyana cewa bai ji dadin yadda Ambasada Damagum ya tsaya kai da fata kan nadin Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyya da kuma soke taron NEC.

Kwamitin na ganin sanarwar da Damagum ya fitar shi kaɗai na mayar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP, da kuma jinkirta ko soke taron NEC, amfani da ofis ne ba bisa ƙa’ida ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng