Wakilan Tinubu da Suka Hada da Minista, Daurawa Sun Isa Madina Jana'izar Dantata
- Wata tawaga daga Gwamnatin Tarayya ta isa birnin Madinah a Saudiyya domin jana'izar fitaccen attajiri, Alhaji Aminu Dantata
- Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya rasu ne a ranar Asabar a Abu Dhabi, kasar Hadaddiyar Daular Larabawa yana da shekaru 94
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an shirya gudanar da jana’izarsa a birnin Madinah, kuma ana sa ran za a yi jana’izar ne a yau Litinin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A safiyar Litinin 30 ga watan Yuni, tawaga ta musamman daga Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta sauka a birnin Madinah na Saudiyya domin jana'izar Alhaji Aminu Dantata,
Fitaccen ɗan kasuwa kuma dattijon Arewa, Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya rasu ne a Abu Dhabi, kasar UAE.

Source: Facebook
Hadimin shugaba Bola Tinubu, Abdulaziz Abdulaziz ya wallafa a Facebook cewa tawagar ta isa Saudiyya ne jim kaɗan bayan barin Najeriya a daren Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yau ake sa ran za a yi jana’izarsa a kasa mai tsarki a Madinah, kamar yadda Musulunci ya tanada.
Dantata: Ministoci, malamai sun wakilci Tinubu
Rahotanni sun nuna cewa tawagar ta haɗa da manyan jami’an gwamnati da fitattun malaman addini.
Shugaban tawagar shi ne Ministan Tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar.
Sauran ‘yan tawagar sun haɗa da Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Lateef Fagbemi, SAN.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama'a, Alhaji Mohammed Idris da Ministan Ƙananan Harkokin Gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata na cikin tawagar.
A cikin tawagar akwai Dr Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Khalifa Abdullahi Muhammad, wanda shi ne limamin Masallacin Dantata dake Abuja.
Najeriya za ta jagoranci jana'izar Dantata
Jakadan Najeriya a Jeddah, Ambasada Muazzam Ibrahim Nayaya, tare da tawagarsa sun kasance a Madinah kafin isowar tawagar daga Najeriya domin shirya dukkan tanade-tanaden jana’izar.
An bayyana cewa za a gudanar da jana’izar ne cikin daraja da mutunci kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Hakan ya biyo bayan kasancewar marigayin mutum ne mai martaba da tarihin jajircewa wajen ci gaban kasuwanci da al’umma.

Source: Twitter
Girmamawa ga rayuwar Alhaji Aminu Dantata
Alhaji Aminu Dantata ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan kasuwa da dattijai a Najeriya, wanda ya taka rawar gani a fannoni da dama na ci gaban tattalin arziki da al’umma.
Rayuwarsa cike take da hidima ga al’umma, taimako da goyon bayan ayyukan alheri a fannoni daban-daban.
Tuni ake ci gaba da aika sakonnin ta’aziyya daga manyan ‘yan Najeriya da ƙungiyoyi, ciki har da shugabannin addini, ‘yan kasuwa da shugabannin ƙasa.
Abba Kabir ya tafi Madina jana'izar Dantata
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya jagoranci tawagar jihar da Jigawa zuwa jana'izar Aminu Dantata a Madina.
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi na cikin wadanda suka tafi Madina domin halartar jana'izar.
Mai martaba sarki, Muhammadu Sanusi II tare da 'yan majalisar fadar sarkin Kano na cikin wadanda suka taka wa Abba Kabir baya zuwa Madina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

